Adalin Sarki , Muhammadu Sanusi II Ka gama lafiya da yardan Allah

0

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jin Kai

Assalamu Alaikum

Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah.

‘Yan uwa masu daraja. Har kullum dai dalilan da suka sa muke nuna kauna da so ga Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II wallahi kara bayyana suke yi ga Al’ummar duniya baki daya, bama na Nigeria kawai ba.

Kai ko babu Komai, Masoyin mu, Mai Martaba Sarkin Kano yayi abunda idan wani ma ya taba yin sa kafin sa, to ni dai ban sani ba. Ku duba fa, ana cikin tafiya a cikin ruwan sama, nan take ya bayar da umurni a cire masa lemar ruwa, ruwa ya taba shi shima, kamar yadda ya ga ruwa suna taba talakawan sa.

Ya ku jama’ah! Wallahi faruwar hakan ya nunawa Al’ummah kafatan cewa shi Sarki ne adali, kuma masoyin talakawan sa da gaske, son da babu karya kuma babu munafunci a cikin sa.

Don haka, wallahi, ya zama wajibi Al’ummah ta so wannan bawan Allah, kamar yadda yake nuna muna kauna, wannan shi zai sa mu rabauta duniya da lahira.

Don haka har kullun muna kara jaddada godiyar mu ga Allah Madaukaki, da yayi muna ni’imar kasancewar sa a matsayin Sarkin Kano.

Mu ci gaba da addu’o’i da fatan alkhairi ga Mai Martaba Sarki. Kar mu yarda da duk wani raini, batanci ko wulakanci zuwa ga re shi.

Daga karshe ina mai rokon Allah da yayi riko da hannun sa, Allah yaci gaba da tsaya masa, ya dafa masa. Allah ya bar Mai Martaba Sarki da Masoyan sa. Allah ya kara masa masoya, amin.

Dan uwan ku, Imam Murtadha Muhammad,
08038289761

Share.

game da Author