HAWAN DAUSHEN LERE: An nada El-Rufai sarautar Yan-Dakan Lere

0

A ci gaba da shagulgulan Babban Sallah da aka gudanar ranar Juma’a a garin Lere, wanda rana ce ta Hawan Daushe, an karrama gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da sarautar Yan-Dakan Lere.

El-Rufai ne mutum na farko da aka yi wa wannan sarauta a wannan masarauta.

Gwamna El-Rufai ya isa garin Lere da misalin Karfe 2 na rana inda saukar sa ke da wuya sai ya garzaya tare da Sarkin Lere zuwa masallacin Juma’a.

Bayan an sakko daga Sallar Juma’a ne aka dunguma sai fadar maimartaba sarkin Lere Abubakar Muhammad II domin Sarki ya karbi jafi daga mahaya, hakimai da masu sarauta sannan kuma a nada gwamna El-Rufai.

An nada gwamna El-Rufai Dan Dakan Lere da misalin Karfe 3:30 na yamma.

A jawabin sa El-Rufai ya ce wannan ziyara da yayi wa masarautar Lere na da muhimmanci matuka saboda karamci da daraja da masarautar ke da shi.

” Na zo garin Lere ne domin in mika gaisuwa ga mutanen wannan gari bisa karamci da suka nuna mana musamman a lokacin zabe da suka gabata. Lere ta taka rawar gani matuka wajen ganin mun samu nasara a zaben jihar.

” Muna taya ku murna da zabe Suleiman Aliyu da kuka yi dan majalisa da Sanata Abdu Kwari Sanatan yankin ku. Gwamnati zata ci gaba da maida hankali wajen samar wa mutanen wannan yanki da ababen more rayuwa kamar yadda ta saba. Ina mai yi muka murna da godiya.

Daga nan El-Rufai yayi alkawarin nada ‘yan asalin garin Lere manyan mukamai a jihar.

A nashi jawabin, Maimartaba Sarkin Lere, Abubakar II ya yaba wa gwamna El-Rufai sannan ya yi masa godiya bisa karrama Lere da mutanen ta da yake yi a jihar. Ya roki gwamna El-Rufai da ya saka baki wajen gyara titin Kaduna zuwa Lere, saboda lalacewa da yayi.

A tawagar gwamna El-Rufai, akwai Mohammed Sani, shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, Sanata Abdu Kwari, Shugaban Hukumar RUWASA, Bashir Umar, Wamban Lere da sauran su.

Share.

game da Author