A San Abubuwa 10 Dangane Da Sabuwar Dokar Gidajen Yari

0

Ranar Laraba ne Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan Dokar Sabunta Tsarin Kurkuku. Hakan ya haifar da canja wa Hukumar Gidajen Kurkuku suna, zuwa Hukumar Gidajen Gyara Halayen ‘Yan Najeriya, ko kuma Hukumar Gidajen Ladabtarwa ta Najeriya.

Akwai Abubuwan Lura Guda Goma Da Suka Hada Da:

1. Sauya sunan Hukumar daga Nigerian Prisons Service zuwa Nigerian Correctional Service.

2. Tun cikin watan Janairu, 2008 ne Sanata Victor Ndoma-Egba ya gabatar da kudirin lokacin ya na sanata. Sai shekaranjiya Laraba aka sa masa hannu ya zama doka.

3. Wannan sabuwar doka ta bai wa Shugaban Kula da Gidajen Kurkuku na kowace jiha ikon kin karbar karin daurarru daga kotu, matukar gidajen kurkukun da ke jihar sun rigaya sun cika makil da daurarru.

4. An raba aikin ma’aikatan gidan kurkuku zuwa bangare biyu. Akwai bangare na farko shi ne na ‘Custodian’ sai na biyu kuma ‘Non-custodian.

5. ‘Custodian za su rika kula da batutuwa da kula da wadanda aka tsare tare da tabbatar da an killace su a wuri ba wulakantacce wanda bai kamata a ajiye mutum ba. Su ne kuma za su kula da ganin cewa an rika gaggauta yanke wa wadanda ke jiran hukunci hukuncin su a kan lokaci.

6. ‘Non-custodian kuma za su maida hankali ne a kan ayyukan yau da kullum na ofis da sauran aikace-aikacen ayyukan da ake sa daurarru na ladabtarwa da duk wani hukuncin da kotu ta yanke a zartas kan wanda ta tsare.

7. Manufar doka da oda shi ne a maida hankali kan gyara halayya da dabi’un mutane, saita wa kangararru kwakwalwa da alkiblar rayuwa da kuma sake karbar su a cikin al’umma bayan sun canja halaye sun zama nagari.

8. Daga yanzu Shugaban Hukumar zai kasance ya na da Mataimaka har guda takwas, a matsayin sa na Controller-General.

9. Za a bijiro da tsari ko manhajar saisaita alkibla da dabi’un wadanda ke tsare, ta hanyar kulawa da lafiyar su, da hankulan su, ba su shawarwari da yi musu nasihohi da wa’azi. Za a rika gudanar da wadannan har ga manyan masu laifi tuburan.

10. Idan wanda kotu ta yanke wa hukuncin kisa ya shafe shekara goma ya na jekala-jekalar daukaka kara, amma bai yi nasara ba, kuma har lokacin ba a zartas da hukuncin kisan a kan sa an kashe shi ba, to Babban Joji zai iya yi masa sasauci ya maida hukuncin sa daga na kisa zuwa daurin rai-da-rai.

Share.

game da Author