‘Yan sanda sun kama dan shekara 15 da ya shirya ayi garkuwa dashi Iyayensa su biya kudin fansa

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Filato ta kama wani ɗan yaro mai shekaru 15 da ya shirya a yi garkuwa da shi da gangar domin iyayensa su biya kuɗin fansa.

Da yake ganawa da manema labarai a garin Jos ranar Alhamis yaron ya bayyana cewa ya aikata haka ne domin samun kudin da sayi kawan sawa na zamani domin wani shagali da abokannan sa suka hada don shima yayi tunkaho.

“ Da gangar na shirya a yi garkuwa da ni. In neman kudi ne domin in sayi sabbin kaya don yin fice a wani shagali da abokanaina suka shirya.

Kwamishinan ‘Yan sandan jihar Isaac Akinmoyede ya bayyana cewa rundunar ta kama mutane hudu da suka hada baki da yaron domin damfaran iyayen sa naira 500,000.

“ Mahaifin yaron ne da kansa ya garzayo caji ofis, inda ya bayyana mana cewa tun da safen ranar dansa ya fita koyon aiki bai dawo ba. Sai daga baya kawai aka kira shi a waya wai ya biya naira 500,000 kudin fansar dansa wai masu garkuwa da mutane ne su kuma sun yi garkuwa da dan nasa.”

Akinmoyede ya ce bayan wannan kara da mahaifin dan ya kawo ofishin ‘yan sanda ne mu kuma muka fantsama aiki. Baya ga wadanda muka kama
sun hada baki da dan wannan mutum, zuwa yanzu ‘yan sanda sun kama Barayi, masu garkuwa da mutane da sauran ‘yan daba har 41 a jihar.

“ Bayan haka jami’an mu sun kama mutane 11 da laifukan yin garkuwa da mutane a kwalejin kimiya da fasaha na Haipang da wasu wurare a karamar hukumar Jos ta Kudu.

Baya ga kama mutane da suka, rundunar ta kwato makamai da dama daga hannu wadannan miyagun mutane.

Share.

game da Author