’Yan bindiga sun kashe kawun Sanata Abbo, sun yi garkuwa da kishiyar mahaifiyar sa

0

Wasu mahara sun yi wa kauyen Muchilla dirar mikiya, su ka arce da kishiyar mahaifiyar Sanata Elisha Abbo, bayan sun bindige kawun sa har lahira.

Maharan dai sun shiga kauyen da ke cikin karamar hukumar Mubi a Jihar Adamawa, a yau Asabar misalin karfe 1 na rana, suka yi garkuwa da matar, wadda mai jego ce, kwanakin ta 11 kadai da haihuwa.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin.

Wani da aka yi kisan da garkuwar a kan idon sa, ya shaida cewa “Yayin da suka tasa keyar matar za su gudu da ita, sai kawun Abbo ya fito ya na kururuwa.”

Wannan ne ya sa ba su tsaya wani bata lokaci ba, suka dankara masa harbi, nan take ya fadi ya mutu.

Yanzu haka dai kauyen ya na cikin tashin hankalin neman inda aka gudu da wadda aka yi garkuwa da ita, da kuma jimamin rashin kawun Abbo.

Kakakin Yada Labarai na Yan Sandan Adamawa, Suleiman Nguroje, ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin.

Sai dai kuma ya ce an tura jami’an su sun shiga binciken yadda za a kubutar da ita da kuma kamo wadanda suka yi kisan da garkuwar.

Sanata Abbo shi ne sanatan da ya gag-gaura wa wata mata mari a kantin saida azzakarin roba, a Abuja, cikin watan Mayu, 2019.

Shi ne sanatan da ya fi dukkan sauran sanatoci karancin shekaru.

Wannan ne karo na farko da aka zabe shi daga Shiyyar Adamawa ta Arewa.

Share.

game da Author