Yadda sojoji su ka yi wa Babban Jami’in Tsaron Sansanin NYSC jina-jina

0

Yanzu haka dai Babban Jami’in Tsaron Sansanin Masu Bautar Kasa na Jihar Ondo, Wale Owolabi, ya na kan gadon asibiti a Akure ya na jiyyar raunukan da sojoji su ka yi masa, a lokacin da su ka rika jibgar sa a cikin harabar sansanin.

Laifin da ya yi musu, shi ne don ya tsaida Kaftin C. U. Kanu da ya kai ziyara cikin sansanin, ya nemi ya binciki motar sa a lokacin da zai fita.

PREMIUM TIMES ta gano cewa Kanu shi ne Kwamandan Sansani wanda ya kula da atisayen masu bautar kasa da aka sallama kafin na yanzu.

Ya kai ziyara ne ga sabon Kwamanda wanda ya maye gurbin sa, mai suna Kaftin Garba.

Yayin da zai fita daga cikin sansanin, sai Babban Jami’in Tsaro, Wale ya nemi ya bude bayan mota domin ya bincika ya gani.

Dama kuma ka’idar ke kanan ko a lokacin da wanda za a bincika din ke kwamandan sansanin, duk wanda zai fita sai an binciki mota, kuma idan dan NYSC ne sai an dauki sunan sa idan zai fita.

LODIN ’YAN MATA A CIKIN MOTAR KAFTIN KANU

Yayin da ya bude motar, sai ya ga kayan NYSC a ciki, na mutum biyu, sannan kuma har da lodin wasu ‘yan mata, ‘yan NYSC su biyu zaune a baya.

Owolabi ya nemi sanin yadda aka yi kayan NUSC ke a cikin motar sa, sannan kuma ya nemi sanin ko su wa ne wadannan ‘yan mata da ya loda, domin a rubuta sunayen su, a san sun fita. Ga shi kuma tsakar dare ne.

Wata majiya ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa maimakon Kaftin din ya yi masa bayani, a wuce wurin, sai ya fara sababi, ya na hayaniya, har sai da aka kai maganar a gaban Ko’dinata na NYSC.

YADDA AKA YI MASA JINA-JINA

A ranar 8 Ga Yuli, bayan Owolabi ya tashi daga aiki a tsakar dare, ya na cikin tafiya kann hanyar gida a motar sa, sai ya fahimci wata motar sojoji kirar Hilux na bin sa a baya, dauke da Kaftin Kanu da kuma wasu girda-girdan sojoji a cikin motar.

“Su ka nemi su sha gaban sa, amma sai ya yi kokari ya juyo a sukwane, zuwa cikin sansanin. Sai su ma suka surnano motar su a cikin sansanin, suka ritsa shi a gaban dandazon ‘yan tireda da ke kasa kayan masarufi a cikin kasuwar sansanin. Suka rika jibgar sa da bulalai na kebur.”

Haka wata majiya daga cikin sansanin ta shaida wa PREMIUM TIMES.

Wata ’yar uwar sa da ta durkusa ta na kuka, ta na rokon su daina dukan dan uwan ta, ita ma ta sha duka. An rika bankadar ta, sannan kuma aka rika gag-gaura mata mari. Haka wani da aka yi abin a kan idon sa ya shaida wa wakilinmu.

Ba su daina dukan sa ba sai da su ka ga sun yi masa jina-jina, kamar yadda aka tabbatar.

PREMIUM TIMES ta ji cewa wannan hargowa da Babban Jami’in Tsaro ya rika yi, sai da ta jawo hankalin Kwamandan Sansanin NYSC da sauran jami’an sansanin.

AN KWANTAR DA SHI ASIBITI

Bayan Owolabi ya ci duka, an kwashe shi ranga-ranga zuwa Asibitin ’Yan Sanda na Alagbaka, inda har yau ya na can ya na fama da jiyya.

Lokacin da wakilinmu ya je ganin kwakwaf a cikin asibitin, ya same shi ba ya iya magana, kuma ana kula da shi. Don haka bai iya yi wa wakilin mu magana ba.

Su kan su iyalan sa da ke zaman jiyyar sa, sun ji tsoron yin magana da dan jarida har a dauki muryoyin su.

Wasu bayanai da PREMIUM TIMES ta samu sun bayyana cewa dama Owolabi na fama da ciwon hawan jinni, to wannan duka da timirmisa shi da sojoji suka rika yi, ta sake dagula masa yanayin jikin sa sosai. Wannan ne aka ce dalilin ci gaba da jiyyar da ke yi, ba a yi saurin sallamar sa ba.

Yayin da PREMIUM TIMES ta tuntubi Jami’in Yada Labarai na NYSC na Jihar Ondo, Bankole Semeon ya shaida wa wakilin mu cewa ana ci gaba da kokarin shawo kan sabanin a tsakanin hukumar sojoji da kuma hukumar NYSC.

Bayan da PREMIUM TIMES ta ji cewa an shigar da korafi a gaban Birgade Kwamanda na Sojoji a Jihar Ondo, sai wakilin mu ya tuntube shi, domin a ji ta bakin sa.

Birgediya Z. L. Abubakar ya shaida wa wakilinmu cewa a bar kaza cikin gashin ta kawai. A bar maganar ba sai an buga a jarida ba, domin NYSC da sojoji za su sasanta a tsakanin su.

Ya ce ko ma dai yaya ta kaya, bangarorin biyu tilas za su ci gaba da aiki tare. Amma a cewar sa, yayata maganar a jarida, za ta iya kawo sabani a tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai kuma ya ki ya bayyana irin matakai ko hanyoyin da za a bi domin hukuntawa ko kashe rikicin.

Share.

game da Author