TARIN FUKA: Najeriya ce ta shida a jerin kasashen da cutar ta addaba – Hukuma

0

Jami’in hukumar hana yaduwar cutar tarin fuka ta kasa (NTBLCP) Ahmad Muhammad ya bayyana cewa bincike ya nuna cewa a jerin kasashen duniyan dake fama da tarin fuka Najeriya ce kasa ta shida.

Binciken ya kuma nuna cewa Najerya na cikin kasashe bakwai a duniya da adadin yawan mutanen dake dauke da cutar ya kai kashi 64 bisa 100.

Wadannan kasashen kuwa sun hada da India, Indonesia, China, Philippines, Parkistan, da Afrika ta Kudu.

Muhammad ya sanar da haka ne a zama da hukumar ta yi domin shirya taron tattaunawa da kungiyoyin bada tallafi na ciki da wajen Najeriya kan hanyoyin da za a bi don dakile yaduwar cutar.

Taron mai taken (Hada kawance da kungiyoyin bada tallafi domin dakile yaduwar tarin fuka a Najeriya) zai gudana ne ranar 17 zuwa 18 ga watan Yuli a Abuja.

Mohammed ya ce ganin yadda yaduwar cutar ke neman ya addabi Najeriya ne ya sa gwamnati za ta handa hannu da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO), USAID, da sauran kungiyoyin bada tallafi domin samar da kudaden da za a bukata wajen kawar da cutar.

“Bincike ya nuna cewa a kason adadin yawan mutanen da ake rasawa a duniya a dalilin wannan cuta, Najeriya da India na da kashi 48 bisa 100’’.

Bayan haka shugaban kwamitin hada kawance da kungiyoyin bada tallafi domin kawar da cutar Lovett Lawson ta ce a lissafe Najeriya na bukatan dala miliya 312 domin kawar da yaduwar cutar nan da 2030.

Lovett ta yi kira ga gwamnati kan kara yawan kudaden da take warewa domin ganin an shawo wann matsala. Bayan haka ta
ce domin cimma wannan buri ya kamata a zo a zauna domin tsara hanyoyin da za su taimaka wajen samar da kudaden da za a bukata wajen dakile yaduwar cutar.

Share.

game da Author