Hukumar kula da ingancin abincin da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta bayyana cewa maganin ‘Avastin Injection’ na iya cutar da kiwon lafiyar mutum idan ba a yi amfani da shi ta hanyar da ya kamata ba.
NAFDAC ta fadi haka ne bayan majalisar dattawa ta umurce ta da ta matsa wajen dakatar da amfani da maganin a kasar nan.
Idan ba a manta ba majalisa ta dauki wannan mataki ne bayan sanata Aishatu Dahiru ta bayyana cewa maganin ya makantar da mutane 10 a asibitin ido na kasa dake jihar Kaduna.
Ta ce an dade ana amfani da maganin ‘Avastin Injection’ domin warkar da cututtukan da ke kama ido sannan a wani binciken da ta gudanar ta gano cewa jaridar ‘NewYork Times’ ta ruwaito cewa wannan magani na makantar da mutum.
Ta yi kira ga gwamnati da ta matsa kaimi a daina shigo wa da wannan magani.
Sai dai kuma bincike ya nuna cewa ana sarrafa maganin ‘Avastin Injection’ ne domin kawar da cutar daji, kawar da cutar sigan dake kama ido sannan da hana rashin iya motsa jiki saboda tsufa.
Amma an gano cewa wasu asibitocin na amfani da wannan magani domin warkar da cututtukan dake kama ido wanda haka bai kamata ba.
NAFDAC ta ce ta tattauna da ma’aikatan asibitin kasa na ido dake Kaduna game da wannan magani sannan ta gudanar da bincike domin tabbatar da inganci maganin da amfanin da ya kamata ya yi a jikin mutum.
Sakamakon binciken ya nuna cewa maganin na da inganci sannan amfani da shi ta hanyoyin da bai kamata ba na iya cutar da kiwon lafiyar mutum.