Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ya nada fitaccen dan jaridan nan, Lanre Lasisi wanda ma’aikacin gidan talabijin din Channels ne kakakin sa.
Baya ga nada Lanre da yayi Kakakin majalisar ya nada wasu masu taimaka masa su biyar.
Wadanda aka nada sun hada da; Musa Abdulahi Krishi – Sakataren yada labarai, Bukola Ogunyemi – mai taimaka masa kan sabbin kafafen yada labarai, Dele Anofi – Mai taimaka masa kan hulda da taridu, Kunle Somoye – mai taimaka masa kan hulda da gidajen talabijin da Radiyo.
Sannan kuma da Ayo Adeagbo mai daukan sa hoto.