A ranar Talata ne Fadar Shugaban Kasa ta kara nanata ikirarin da ta ke yawan yi cewa tuni an murkushe Boko Haram.
Wannan matsaya da Fadar Shugaban Kasa ta dauka ta na kunshe ne a cikin wani bayani da Kakakin Yada Labarai na Shugaba Muhammadu Buhari, Garba Shehu ya bayar.
“ Matsayar wannan gwamnati ita ce an kakkabe Boko Haram, kuma an murkushe su. Tantagaryar ’yan Boko Haram da muka sani dai yanzu an gama da su.” Inji Shehu, a cikin wata takardar da ke kunshe da bayanan da ya turo wa PREMIUM TIMES a jiya Talata.
Bayanan Shehu sun zo ne kwanaki uku bayan da Boko Haram suka kai hari a wani kauye a jihar Barno, har suka kashe masu zaman makoki mutum 60, kuma da dama suka ji raunuka.
Sannan kuma a cikin watannin baya sun kashe sojoji a Barno, Yobe da Adamawa.
Sun kuma yi garkuwa da mutane da dama a kwanan nan, ciki har da ma’aikatan agaji su shida da aka yi garkuwa da su a tsakiyar watan Yuli, kuma har yanzu su na can a tsare.
Shehu ya ce, “ Yanzu babu Boko Haram, sai dai wasu rikakkun ‘yan ta’adda da kuma masu rajin ‘jihadin kafa shari’ar Musulunci a kasashen Magrib, wadanda suka hade da na Afrika ta Yamma suke guma ta’addanci a kasar nan.”
Sai dai kuma jama’a da dama na ci gaba da caccakar gwamnati, su na cewa yaudara ce kawai idan ta na cewa ta kakkabe Boko Haram.
Shehu ya kara jaddada cewa an samu zaman lafiya tare da murkushe Boko Haram idan aka yi la’akari da yadda Gwamnatin Buhari ta samu kasar nan a farkon hawan mulkin ta.
Ya ce a yanzu an daina kai hare-hare a Arewacin kasar nan, sai dai can kan iyakokin gabas da ke makautaka da kauyukan da ke cikin surkukin lungu.
Wannan bayani dai ya zo ne a daidai lokacin da rikicin Boko Haram ya cika shekara 10 daidai. Wato daga jiya Talata, 30 Ga Yuli ne aka cika shekara 10 da barkewar rikicin da ‘yan sanda a Maiduguri suka kashe Mohammed Yusuf, shugaban Boko Haram.
Tun daga lokacin mabiyan sa suka yi rantsuwa cewa ba su yafe ba, ba za su yafe ba, kuma sai sun rama.