Matawalle zai dauki sabbin ma’aikata 8000 aikin gwamnati a jihar Zamfara

0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kammala shiri tsaf domin daukan sabbin ma’aikata 8000 a jihar.

Matawalle ya ce tuni har gwamnatin sa ta tara kudaden da zata rika biyan sabbin ma’aikatan.

” Wadannan sabbin ma’aikata da za mu dauka bai hada da matasa 1,400 da gwamnatin da ta wuce ta dauka ba sannan ta kasa biyan su har na tsawon shekaru 2 ba. Zuwa yanzu na ce a je a tantance wadannan mata. Wadanda har yanzu basu da aikin yi, kuma basu koma makaranta ba, su dawo mu ci gaba da aiki da su a gwamnatin jihar.”

” Bayan haka gwamnati ta ware naira Miliyan 150 domin tallafawa wa mata 7,500 a jihar. Zamu zabi mata 1500 daga duk fadin jihar mu rika biyan su naira 20,000 a kowani wata domin inganta sana’o’in su.

” Bayan haka mun samu tallafin tireloli 50 na takin zamani daga gwamnatin tarayya domin manoman mu. Sannan ina so in tabbatar muku da cewa gwamnati na ta jama’a ce kuma za mu tabbata an ciyar da jihar Zamfara gaba kamar yadda muka daura damarar yi.

Share.

game da Author