Gwamnatin Tarayya ta fara wani gagarimin shirin daukar dimbin tsoffin sojoji aiki tare da iyalan su da ma sauran ba’arin jama’a ga duk mai sha’awa.
Wata majiya a cikin hukumar tsaro ta sojoji ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa an amince da fara daukar su ne a cikin wannan makon. Kuma tuni aka fara wannan dauka aikin a fadin kasar nan.
An kafa wasu jami’ai na daukar tsoffin sojojin masu bukatar karin kudaden shiga baya da fanshon da suke karba a duk wata. Haka PREMIUM TIMES ta samu labari, kuma ta tabbatar.
An umarci mahukuntan sojoji kasa, na sama da na ruwa su rarraba fam a dukkan ofisoshi da barikokin su a fadin kasar nan, domin a dauki jami’an da suka yi ritaya, a ba su aiki kwatankwacin na Jami’an Tsaron ‘Corps Commissionaires’ na Birtaniya.
An kirkiro shirin domin a samu hanyoyin rage radadin rashin aiki yi a kasar nan, wanda ya kara muni sosai cikin shekaru hudu sakamakon yawan korar ma’aikata. A gefe daya kuma milyoyin matasa na zaune turus babu aikin yi.
Sai dai kuma ba a san ko guda nawa ne za a dauka a fadin kasar nan ba. Amma dai ana sa ran za a tura mafi yawan su ne yin gadi ma’aikatu, cibiyoyi da hukumomin gwamnati.
Kakakin Ma’aikatar Tsaro, Onyema Nwachukwu bai dauki waya ba, yayin da wakilin mu ya kira shi domin jin ta bakin sa a yau Laraba da safe.
Wata kididdiga ta nuna cewa gwamnatin tarayya ya zuwa 2018 ta dauki matasa 500,000 aiki, baya kuma ga tsarin N-Power da ake cin moriyar sa.
Discussion about this post