Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa akasarin rikice-rikice da kashe-kashen da ke faruwa a kasar nan, duk ’yan siyasa ne malaman addini ke haddasa su.
Buhari ya yi wannan kakkausan zargi a lokacin da ya ke gabatar da jawabi a Dandalin Eagle Square, domin Ranar Tunawa da Cikar Dimokradiyya shekaru 20 da sake kafuwa a Najeriya.
Buhari ya kuma ce dukkan wannan matsalar rashin tsaro malaman addini ne da kuma shugabannin siyasa ke haddasa su, domin su gurgunta kasar nan.
“Yawancin rikice-rikicen kabilanci da na addini, duk sun a faruwa ne sanadiyyar kalaman ruruta wutar kiyayya da shugabannin siyasa da addini ke shugabannin siyasa da malaman addinai suke watsawa.
“Su na yi ne domin neman biyan bukatun su ta hanyar gurgunta kasar nan da haddasa gaba da kiyayya da raba kan jama’a.”
“Majalisar Dinkin Duniya ta ce nan da shekara ta 2050, yawan al’ummar Najeriya za su kai milyan 411, kenan za mu zama kasa mafi yawan jama’a ta uku bayan Chana da kuma India.”
Daga nan sai Shugaba Buhari ya ce zai tabbatar da cewa Najeriya ta kasance kasa daya dunkulalliya mai ingantaccen hadin kai da kaunar juna.
Buhari ya bada labarinnirin sadaukar da rayuwar sa da ya yi a kan Najeriya.
Ya ce: “Mu na kuma sane da cewa akwai dangantaka tsakanin rashin daidaiton tallalin arziki da kuma matsalar rashin tsaro.
“Ta’addanci ya zame wa duniya baki daya alakakai, ta yadda har manyan kasashen da suka bunkasa sosai ma su na fama da ta’addanci da tashin zaune tsaye, ta yadda su ke ta gaganiyar neman kawar da wadannan matsalolin.
Buhari ya ce mu a kan za a iya kawar da wannan matsalolin ta hanyar kafa ayyukan raya kasa da na inganta rayuwar jama’a.
Daga nan sai ya amince da cewa hare-haren samame da kuma garkuwa da mutane sun zame wa gwamnatin sa sauran kalubalen da suka yi wa gwamnatin sa barazana a shekaru hudun da ya yi.
Ya tuna wa jama’a cewa a lokacin hawan mulkin sa na farko, hare-haren Boko Haram sun yi kamari ta yadda su ke kai harin bama-bamai a kowane birni ko kauye a kasar nan. Ciki har da Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya a nan Abuja.
Daga nan sai ya ce amma yanzu duk an dakile wannan faffaka da Boko Haram suka rika yi gaba-gadi cikin kasar nan.
Da ya koma a kan zangon na biyu kuwa, Buhari ya jaddada alwashin sa wajen ganin ya magance matsalolin da suka addabi kasar nan.
Discussion about this post