An hukunta mutane 1,234 cikin shekara hudu – Inji EFCC

0

An kiyasta cewa akalla an EFCC ta gurfanar kuna kotu ta hukunta mutanec 1,234 tun daga 2015 zuwa yau.

Shugaban Hukumar EFCC Ibrahim Magu ne ya bayyana haka a ranar Talata da ta gabata.

Magu ya kara da cewa ‘yan Najeriya sun kasance cikin ukubar abin da ya kira “manyan da suka kankane komai”, ta hanyar murde zabe da kuma amfani da kudaden sata domin su danne hakkin wanda al’umma suka zaba.

Da ya ke magana a wurin Taron Yaki da Rashawa, a jajibirin Ranar Dimokradiyya a Abuja, wanda aka gudanar a otal din Sheraton, Magu ya ce a cikin 2015 an hukunta mutane 103, wasu 194 cikin 2016, sai 189 cikin 2017 sai kuma 312 a cikin 2018.

Ya kara yin bayanin cewa daga watan Janairu, 2019 zuwa yau, an hukunta mutane 406, sannan an kwato dimbin dukiyoyi na bilyoyin nairori.

Shugaban na EFCC ya ce rashawa ba wai a kan tattalin arziki kawai ta yi illa ba. Ya ce ta samu gindin zama wajen yakar ta’addanci.

Ya ce hujjoji bayyanannu da kuma binciken da masana suka gabatar ya tabbatar da cewa cin hanci da rashawa sun karya lagon ingancin dimokradiyya a kasar nan a cikin shekarun da suka gabata.

Ya ce EFCC ta yi rawar gani a zaben 2019, inda ta rika sa-ido ta na kama dillalan saye da sayar da kuri’u kuma ta na gurfanar da su a gaban kotu.

Ya ce jam’iyyun siyasa sun rika sayen ‘yancan masu zabe da kudi, saboda sun san ba su da wani nagartaccen tsarin ciyar da su gaba da gare su.

Cikin wadanda suka halarci taron har da Shugaban Kasar Rwanda Paul Kigame, Jakadan Amurka a Najeriya, Stuart Symington, Shugaban Tawagar Kungiyar Turai, Ketil Karlsen da wasu gwamnonin Najeriya.

Share.

game da Author