Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta dage sauraren karar da dan takarar PDP, Atiku Abubakar da PDP din suka kai inda suka kalubalanci sakamakon zaben.
An dage saurarenn shari’ar zuwa ranar 1 Ga Yuli, wadda suka kalubalanci zaman kotun na 11 Yuni.
Kotu ta dage sauraren karar bayan da lauyan PDP Chris Uche ya shigar da uzirin kalubalantar abin da ya wakana a ranar 11 Ga Yuni.
A waccan rana dai APC ta nemi a kori karar da PDP ta shigar saboda wadansu dalilai masu tankiya.
Ita kuma PDP ta sake shigar da batun kada a kori karar da ta shigar, domin akwai batutuwa makil a ciki wadanda kotu ya kamata ta duba.
APC ta yi zargin cewa wani lauya ne ya sa hannu a karar da PDP ta shigar wanda ba lauyan Mista Uzuegwu ba.
Atiku da PDP sun ki amincewa da sakamakon zaben 2019, wanda Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC ta bayyana cewa dan takarar jam’iyyar APC, Shugaba Muhammadu Buhari ne ya yi galaba a kan na PDP, Atiku Abubakar.
A na sa bangaren, Atiku ya yi ikirarin cewa shi ne ma ya yi nasara, ba Buhari ba.
Ya yinzargin cewa INEC ta baddala lissafin alkaluman zaben ta yadda ta jirkita nasarar a kan Buhari.
Atiku ya yi zargin cewa sakamakon zaben ainihi da INEC ta tattara a cikin rumbun tara alkaluman kidayar kuri’u, wato ‘server’, ya nuna cewa shi ne ya yi nasara.
Amma kuma sai ita INEC din ta fitar da alkaluma na boge, kamar yadda Atiku ya yi zargi.
INEC ta karyata cewa ta mallaki ‘server’. Sannan kuma a yanzu kotu ta soke batun neman da Atiku ya yi cewa ta ba shi iznin binciken ‘server’ din da ya yi ikirarin cewa akwai.