ZAMFARA: Ban bar wa Zamfara bashi ko na kudin daddawar miya ba –Yari

0

Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Abdul’aziz Yari, ya bayyana cewa bai bar wa jihar bashi ko na kwandala ba a lokacin da ya sauka bayan kammala zango biyu na tsawon shekaru takwas da ya yi.

Yari ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi wurin taron manema labarai a hedikwatar jam’iyyar APC da ke Gusau, babban birnin Jihar.

Yari, wanda kakakin yada labaran sa Ibrahim Dosara ya wakilta, ya jaddada cewa bai bar wa gwamnatin sabon gwamna Bello Matawalle bashin ko kwandala ba, kuma bai bar sauran kudaden ‘yan kwangila da bai biya ba.

An gudanar da wannan taron manema labarai ne a jiya Laraba.

“Ina so na fito baro-baro na shaida muku cewa tsohon gwamna Abdul’aziz Yari bai bar bashi ko guntun biyan kudade ba kafin ya sauka daga mulki ya mika wa Bello Matawalle.

“Taron manema labarai da tsohon mataimakin gwamna, Alhaji Ibrahim Wakkala ya gabatar inda ya ce Yari ya bar kwantai din bashi na naira bilyan 251, ba gaskiya ba ce, an karkatar da hankalin jama’a ne kawai, kuma an yi ne domin a ci mutuncin tsohon gwamnan.

“Mu na mamakin yadda kwamitin da ya ce an bar wannan bashi kuma ya kasa bayyana wa duniya cewa Yari ya bar zunzurutun kudi har naira bilyan 7 a cikin asusun gwamnatin jihar Zamfara.

“Sannan kuma sun kasa bayyana wa jama’a cewa tsohon gwamnan ya shimfida kwalta ta daruruwan kilomita a dukkan Kananan Hukumomin Jihar Zamfara 14. Ga kuma sauran ababen more rayuwar mulkin dimokradiyya masu yawa da ya samar wa jihar ta Zamfara.” Inji shi.

Ya ci gaba cewa “kai ko a batun bayar da kwangiloli, ya kamata tsohon mataimakin gwamnan ya sanar da ‘yan jarida cewa ba tsohon gwamnan ba ne ke bayar da kwangiloli, domin akwai shugaban kwamitin bayar da kwangiloli, wanda akin sa kenan.”

Dosara ya zargi Wakkala da cewa shi ne ma ya yi wa “shirin biyan garatutin ma’aikata na naira bilyan 2 kafar-ungulu, saboda ana cirar kudaden ne daga kudaden biyan takin da manoma ke biya. Saboda kuma manoma da yawa na kukan cewa aika-aikar da Wakkala ya rika yi ta hana su samun takin domin gonakin su.”

Kakakin Yada Labaran wanda ya je wurin taron manema labarai tare da shugaban jam’iyyar APC na Jihar Zamfara, Lawali Liman, har da tsoffin kwamishinoni da manyan jami’an APC na jiha.

Ya yi kira ga gwamnatin PDP ta jihar Zamfara da kada ta dauki aniyar yi wa gwamnatin da ta shude bi-ta-da-kulli.

Maimakon haka, Dosara ya ce kamata ya yi wannan sabuwar gwamnati ta kama turbar ciyar da Jihar Zamfara gaba.

Share.

game da Author