Hadiza ta roki Kotu ta raba aurenta da Usman

0

Ranar Litini ne kotu a Gudu dake babban birnin tarayya Abuja ta bukaci wata matan aure mai suna Hadiza Bala da ta gabatar da shaidu akalla biyu da ke da kwararran hujoji cewa wai mijin ta na ci mata mutunci a zaman auren su.

Sai dai kuma bayan ta kawo wadannan mutane biyu Alkalin kotun Ado Muktar ya kori shaidun biyu cewa basu bayyana hujjoji da su ka gamsar da kotu ba.

Muktar ya daga shari’ar ranan 11 ga watan Yuli.

Hadiza mai shekaru 14 ta shigar da kara a wannan kotu ranan 14 ga watan Yuni tana neman kotu ta raba aurenta da mijinta Usman saboda cin zarafinta da yake yi.

Ta ce baza ta iya komawa gidan Usman ba domin tana tsoron kada wata rana ya kashe ta.

“Kullum Usman kan ci zarafina da haka ya sa nake bukatan na rabu da shi.

Quadin Ibrahim daya daga cikin shaidun da ta gabatar ya bayyana cewa wata rana ya ga lokacin da Hadiza ta fito daga dakin ta zindir haihuwar uwarta da gudu.

Ibrahim yace washe gari ya ga iyayen Hadiza sun zo sun tafi da ‘yar su.

Share.

game da Author