Cewa wai goggon biri ya hadiya miliyan 6 a Kano zuki tamallen ‘yan jarida ne – Ganduje

0

Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa labarin da ake ta yadawa wai goggon biri ya hadiya miliyan 6.8 a gidan ajiye namun daji na Kano zuki tamallen ‘yan jarida ne.

Ganduje ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa.

” Mun umarci hukuma ta binciki wannan magana. An gano cewa ashe barayi ne suka far wa gidan Zoo din, suka sace kudaden amma ba goggon biri ba, domin babu ma goggon biri a wannan gidan ajiye namun daji.

Daga nan sai Ganduje ya ce babban makasudin ziyartar sa fadar shugaban kasa shine don yayi masa bayani game da matakan da jihar ta dauka game da tsaro a jihar.

Da ya ke amsa tambaya game da maganar sulhu tsakanin sa da sarkin Kano Muhammadu Sanusi Ganduje ya ce haryanzu ana a matsayin sulhu ne a tsakanin su. Amma babu maganar wai shi ya kafe sai an tsige sarkin.

Share.

game da Author