KIRKIRO MASARAUTU: Masu ikon zaben sarki a Kano sun maka Ganduje kotu

0

Masu ikon zaben sarki a Masarautar Kano su hudu, sun maka Gwamna Abdulahi Umar kotu, bisa rashin amincewar su da kirkiro sabbin masarautu da ya yi.

Hakan ya biyo bayan nada Sarakuna ne wanda yin hakan ya dora sabbin sarakunan a kan su, domin su hakimai ne, ba sararakuna ba ne.

Sauran wadanda aka hada tare da Ganduje aka maka kotu, sun hada da Kakakin Majalisar Jihar Kano, Kwamishinan Shari’a na Kano da kuma sabbin sarakuna hudu da Ganduje ya nada:

Sabbin sarakunan sun hada da Tafida Abubakar Ila, Ibrahim Abdulkadir, Abrahim Abdulkadir ll da kuma Aminu Ado Bayero
Wadanda suka maka su kotun, su na Manyan Hakiman Kano masu ikon zaben sarki a Kano, wato Madadkin Kano, Hakimin Dawakin Tofa, Yusuf Nabahani; Makaman Kano, Hakimin Wudil, Abdullahi Sarki Ibrahim; Sarkin Dawaki Mai Tuta, Hakimin Gabasawa, Bello Abubakar da kuma Sarkin Ban Kano, Hakimin Dambatta, Muktar Adnan.

Sammacen karar wanda aka shigar jiya Talata kuma ya zo hannun PREMIUM TIMES, masu zaben sarkin sun nemi kotu ta jingine nadin sarautun da gwamnan ya yi tare da yin watsi da Kwaskwarimar Dokar Nadin Sarauta da Karin Masarautu ta 2019 da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi.

Sammacen ya nemi a hana sabbin sarakunan hudu na Gaya, Karaye, Rano da Bichi gudanar da aikin su a matsayin sabbin sarakuna.

Sun nuna cewa Masarautar Kano ta na da dadadden tarihi fiye da shekaru 1000 da suka gabata, tun 999AD. Bayan da Fulani suka yi Jihadi a 1804, da kuma cin birnin Kano da yaki a 1807, sai kasar Kano ta zama karkashin Sarki daya.

Takardar karar da aka shigar ta ci gaba da cewa: “Wadanda suka shigar da kara su ke da alhakin zaben sarki a Kano, kuma kowanen sun a wakiltar wani jinsi ne na Fulani, kamar Yolawa, Jobawa, Sullubawa da Dambazawa. Su ne ke zaben sarakuna, kuma su ne ke kula da yankuna daban-daban na cikin Marautar Kano.

“Wadanda ake karar sun yi gaggawa da azarbabin zartas da hukuncin kirkiro sabbin masarautun Bichi, Karaye, Rano da Gaya, ta hanyar daddatsa Kano a cikin fushi da gilla, ba tare da yin la’akari da bin ka’idar da ta dace a bi ba. kuma ba tare da yin la’akari da gurbata tarihi da wannan kasassaba za ta haifar ba.

Wadanda suka shigar da karar sun dauki manyan lauyoyi (SAN) har guda bakwai da za su bi musu shari’ar a kotu. Akwai kuma sauran lauyoyi 21.
Cikin manyan lauyoyin har da A.B Mahmood da Paul Usoro.

Duk da cewa Babbar Kotun Jihar Kano ta hana Ganduje bai wa sarakunan sandar mulki, ya yi biris da umarnin, inda ya damka wa su hudun sandunan mulki a cikin dare.

Gwamnatin Jihar Kano ta kafe kan cewa takardar umarnin kotu ba ta same ta ba sai bayan bada sandar mulkin.

Share.

game da Author