NCDC ta hada hannu da RKI domin samar da kiwon lafiya na gari a Najeriya

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka na kasa (NCDC) da cibiyar gudanar da bincike da hana yaduwar cututtuka ta kasar Jamus (RKI) sun rattaba hannu a takardar yarjejeniyar samar da kiwon lafiya na gari a kasar nan.

NCDC ta yi hakane ganin cewa RKI na da kwarewar da zai taimaka wa fannin kiwon lafiyar kasar nan.

RIK za ta tallafa wa NCDC da kwarewar da suke bukata domin samun nasarar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya.

Idan ba a manta ba fannin kiwon lafiyar kasar nan ta yi fama da cututtuka da suka hada da zazzabin lasa, bakon dauro, sankarau, monkey pox, ebola da sauran su da a dalilin haka mutane da dama suka rasa rayukan su.

Bayanai sun nuna cewa rashin samun kwarewar dakile yaduwar cututtuka da fanni na daga cikin matsalolin da ya sa wasu cututtukan kamar su zazzabin lasa da Monkey pox suka iya tsallakawa zuwa kasashen waje daga Najeriya sannan wasu cututtukan kamar su monkey pox suka shigo kasar daga kasashen waje.

A karshe jami’in RKI Lothar Wieler ya ce yana da tabbacin cewa tallafin da za su samar wa Najeriya zai taimaka wajen samar da kiwon lafiya mai nagarta a kasan.

Share.

game da Author