Mahara sun kashe mutane uku a Kaduna – ‘Yan sanda

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta bayyana cewa mahara sun kashe mutane uku a kauyen Unguwan Rimi dake karamar hukumar Kauru.

Jami’in hulda da jama’a Yakubu Sabo ya sanar da haka ranar Talata da ya ke zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kaduna.

Sabo ya ce maharan sun far wa kauyen da karfe 2:25 na ranar Litini inda suke ta harbi ta kota ina.

Harbin da maharan suka yi ya yi ajalin yara uku wanda a ciki akwai Monday Yahaya mai shekaru 8, Samson David mai shekaru 17 da Ashimile Danlandi mai shekaru 9.

Sabo yace nan da nan rundunar ta aika da dakaru domin kawo wa kauyen dauki.

Bayan haka Dagacin Chawai Res-Tsam Yahaya Mohammed ya tabbatar da haka inda ya kara da cewa maharan sun zarce zuwa kauyen Chikoba dake kusa da su da karfe hudu na yamma ranar.

Mohammed ya ce a kauyen Chikoba maharan sun harbe yaro daya sannan wani tsoho ya samu rauni.

Share.

game da Author