Tilas sai Najeriya ta jajirce yin ajiya a Asusun Tara Rarar Ribar Danyen Mai – Ministar Kudi

0

Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa ya zama tilas Gwamnati ta jajirce wajen maida hankali ta na tara rarar ribar danyen man fetur a cikin Asusun Hukumar Tanadin Kudaden Zuba Jari (NSIA).

Ta ce hakan ya zama wajibi, domin samun damar ci gaban inganta asusun ganin yadda a karo na shida kenan cikin shekaru biyar da kafa NSIA ana sanar da irin ribar da ake samu.

Ministar ta yi wannan jawabi ne ranar Alhamis a lokacin da ta ke ganawa da manema labarai, irin wanda ta kan shirya duk bayan wata uku domin sanar da ci gaban da Ma’aikatar Harkokin Kudade ke ciki.

Ta ce gwamnati na aiki domin ganin Majalisar Bada Shawara kan Tattalin Arziki (NEC) ta tabbatar da cewa ta na tanadin kudaden Rarar Ribas Danyen Mai domin karfafa NSIA da kudaden da ake tarawar.

“Hakikanin gaskiya NSIA na matukar kokarin ganin ta na ririta Asusun nan na ‘Stabilisation Account’, wanda ke hana gwamnatoci tagayyara a ranar da aka samu akasin rashin wadatar kudaden shiga.

” Amma Ma’aikatar Harkokin Kudade na fatan za ta samu fahimta tsakanin ta da Majalisar NEC, wadda Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ke shugabanta, domin kara jan hankalin dukkan gwamnonin jihohin mu 36 har da Babban Birnin Tarayya, FCT domin su kara himma wajen kara yawan kudaden da ake tarawa a Asusun Rarar Ribar Danyen Mai (ECA).

“Saboda akwai wata doka ko gargadi zan ce a cikin ka’idojin NSIA da ta jaddada cewa gwamnati ta jajirce a koda yaushe ta na samar wa NSIA kudaden da suka kamata daga asusun ECA, amma ba a iya cimma wannan bukata ba har zuwa yau.

“Ba abu ne da gwamnatin tarayya ita kadai za ta rika yi ba, saboda Asusun ECA na gwamnatocin tarayya, jihohi ne da kuma kananan hukumomi.

Dama kuma a farkon wannan wata sai da Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya yi korafi a kan yadda Najeriya ba ta daukar Asusun Inganta Jarin Tattalin Arziki (SWF) da muhimmanci.

Share.

game da Author