Kullum Kwarjinin Siyasar Najeriya Raguwa Yake A Idon Talakawa, Daga Mustapha Soron Dinki

0

Tun bayan dawowar siyasa a jamhuriyya ta hudu, a 1999, mutane sun samu farin ciki sosai saboda an dade ba a hadu ba shiyasa mutane suka fito sosai don samar da shugabanci a bangarori da dama.

Obasanjo a matsayin shugaban kasa na farko a jamhuriyar, yayi kokari matiqa wajen rainon dimokradiyya har ta kai zango biyu a hannunsa ba tare da soja ya sake yin juyin mulki ba kamar yadda aka saba yi.

Mustapha Soron Dinki

Mustapha Soron Dinki

Siyasa ta samu kar6uwa ne a wancen lokacin, mutane sun so ta duk da bata fara gudanuwa ba balle a gwada nauyin cigaban da ta kawo.

Tabbas, siyasa a lokacin ta samu abun da ake kira da ‘intrinsic legitimacy’ tunda anyi murna da ita tun kafin a sha romonta saboda an gaji da mulkin soja.

A kwana a tashi, ashe an gudu ba a tsira ba duba da yadda siyasar take samun koma-baya yanzu saboda rashin shugabanci na gari da tsaro da kuma halastaccen zabe.

A binciken da Afro-Barometers suka yi a shekara ta 2000, ya bayyana cewa a wannan lokacin siyasa ta samu goyon baya da yabo 80%, a shekara ta 2005, soyayyar ta koma 65%, ta sake sauka zuwa 47% a shekara ta 2015 (Afro-barometer briefing paper 2000, 2006 and 2010).

Tabbas, daga kan shekara ta 2015 zuwa yanzu Allah ne yasan mutanen da suka yankewa kansu hukuncin daina yin zabe saboda sun samu ‘crisis and frustration of expectations’. Ko a zabukan da aka yi baya, mutane igiyar zato ce tasa suka yi zabe.

Duk sanda gwamnati ta samu abun da ake kiransa da ‘legitimacy crisis’ to gaskiya ta samu matsala.

Misali, a siyasar Najeriya ne ake fifita bukatar mutum daya kacal akan ta talakawa, ake bawa bukatar jam’iya mahimmanci akan ta gwaunati, sannan ake fifita bukatar masu mulki akan ta wadanda ake mulka.

A duk lokacin da gwamnati ta rasa kan-gado, ta koma bagidajiya, tana yin abubuwan da basa kan layin cigaban talakawa, to lallai abun saidai a bishi da Innalillahi Wa’inna Ilaihi Raji’un. Sannan ba zata ta6a dorewa ba.

Ina bawa gwaunati shawara akan yin abun da ya dace idan har ana neman dorewar Dimokaradiya a Najeriya. Talakawa sun cika da bakin ciki sakamakon rashin samun tsaro na rayuwa har yanzu (life security).

Allah ya shiryar damu.

Share.

game da Author