Gwamnatin jihar Kogi ta sanar cewa mutane hudu sun kamu da zazzabin lassa a jihar sannan biyu daga cikin su sun riga mu gidan gaskiya.
Kwamishinan kiwon lafiya Saka Audu ya sanar da haka a taron wayar da kan mutane kan hanyoyin kawar da ambaliyar ruwa, kamuwa da zazzabin lassa da sauran cututtuka da ake kamuwa da su a dalilin rashin tsaftace muhalli.
Audu ya ce an fara gano alamun cutar a jikin mutane 10 inda bayan gwaji aka samu tabbacin mutane hudu na dauke da cutar.
” Daga cikin mutane hudu din dake dauke da cutar biyu sun rasu sannan biyu sun sami sauki.
” Sakamakon binciken da muka gudanar ya nuna cewa mutanen uku daga karamar hukumar Ibaji suke sannan daya daga karamar hukumar Ijumu.
Audu ya yi kira ga mutane kan kiyaye matakan kawar da cutar domin guje wa kamuwa da cutar.
Bayan haka darektan ma’aikatan kiwon lafiyar jama’a Frances Akpa ya bayyana cewa gwamnati ta shirya wannan taro ne domin samun makawa daga ambaliyar ruwa,zazzabin lasa da cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin rashin tsaftace muhalli.
Akpa ya ce idan ba a manta ba a 2018 jihar kogi na daya daga cikin jihohin kasar nan da ta fi harbuwa da zazzabin lassa.
Ya ce domin gujewa fadawa irin haka gwamnati ta yi tanadin magunguna, horas da ma’aikatan kiwon lafiya sannan da wayar da kan mutane kan hanyoyin gujewa kamuwa da cututtuka.
Hanyoyin guje wa kamuwa da zazzabin lassa.
1. Da zarar mutum ya kamu da zazzabi a tuntubi likita domin tabbatar da cutar da mutum ke dauke da shi.
2. Duk ma’aikacin kiwon lafiya da zai duba mara lafiya a asibiti ya tabbata yana sanye da safar hannu sannnan ya kuma tabbata ya wanke hannayen sa da kyau bayan ya gama duba mara lafiya.
3. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbatar sun nemi magani da zarar alluran da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
4. A tabbata an tsaftace muhalli da kuma adana kayan abinci nesa da fitsari da kuma kashin beraye.
5. Ba a iya kamuwa da cutar zazzabin Lassa idan an taba wanda ke dauke da cutar amma za a iya kamuwa da shi idan yawu, jini ko kuma zufan wanda ke dauke da cutar ya taba wanda ba ya da shi