Sabon shugaban hukumar kula da masu yi wa kasa hidima (NYSC) Shuaibu Ibrahim ya bayyana cewa zai maida hankali wajen ganin masu yi wa kasa hidima suna samun tsaro da kariya ga rayukan su a kowani lokaci.
Ibrahim ya fadi haka ne a ziyara da ya kai ofishin hukumar dake Akure a jihar Ondo.
Ya ce ya dauki matakan da za su taimaka wajen samar da jari wa duk dan bautan kasan da ya dauki horon fara sa’anar hannu da daraja da hukumar ke yi.
” A shirin horas da masu yi wa kasa hidima sana’o’in hannu SAED, NYSC ta hada hannu da kamfanoni domin samar da jari ga duk wanda ya nuna kwazo da himma a aiki.
Ibrahim ya kuma ce a fannin kare rayukan masu yi wa kasa hidima a shirye yake da ya sadaukar da nasa ran don samar musu da haka.
” Ina kira gare ku da ku nisanta kan ku da yanwon banza ku yi amfani da wannan dama domin banbanta kanku da sauran mutane yayin da kuke yi wa kasar ku hidima.”