Sakamakon binciken da kungiya mai zaman kanta na ‘Project Pink Blue’ ta gudanar ya nuna cewa kashi 82 bisa 100 na maza a Najeriya basu yin gwajin cutar dajin dake kama ‘ya’yan maraina.
Jami’in ‘Project Pink Blue’ Runcie Chidebe ya sanar da haka a taron wayar da kan mutane kan cutar da akayi suka a Abuja.
Ya kuma kara da cewa rashin sani,rashin gwajin cutar da tsadan magani na daga cikin dalilan dake kisan maza a Najeriya.
Chidebe yace wayar da kan maza game da cutar don kiyaye hanyoyin kamuwa da cutar,tilasta wa kowani namiji yin gwajin cutar,rage farashin magani zai taimaka waje hana yaduwar cutan.
Dajin dake kama ‘ya’yan maraina
Likitoci sun ce wannan cuta na kama maza masu shekaru 40 zuwa sama. Sannan bincike ya nuna cewa bakaken fata yan Kasashen Afrika musamman masu shekaru 40 sun fi fama da cutar.
Alamun cutar sun hada da rashin iya yin fitsari yadda ya kamata,yin fitsari da jini,ciwon kirji da sauran su.
Sannan shan taba,shan giya na daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar.
Zuwa asibiti domin yin gwajin cutar sau daya a shekara domin gano cutar da wuri, cin kayan lambu da ‘ya’yan itatuwa na hana sa a kamu da cutar.
Abubuwa 8 da ya kamata a sani game da cutar.
1. Cutar ya fi kama bakaken fata maza a duniya.
2. Ana iya gadon cutar.
3. Cutar baya hana karfin mazakutan namiji.
4. Zuwa asibiti domin yin gwajin cutar na cikin hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.
5. Cutar ya fi kama maza daga shekaru 40 zuwa sama.
6. Rashin iya fitsari da yin fitsari da jini na cikin alamun cutar.
7. Shan tabar sigari, giya na iya kawo cutar.
8. Cin ‘ya’yan itatuwa kamar su tufa da ganyayakin da ake ci na hana kamuwa da cutar.
Discussion about this post