Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa sam-sam bai ji dadin yadda mu’amularsa ta kasance da majalisar dokoki ta kasa ba karkashi shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da na Wakilai, Yakubu Dogara.
Buhari ya fadi haka ne a gayyatar shan ruwa da yayi wa shugabannin majalisar yau a fadar gwamnati.
” Ina fatan majalisa mai zuwa zai fi wannan da ke yi mana bankwana. Aikin majalisa shine a hada hannu da fannin zartaswa domin yi wa kasa aiki amma a gaskiya akasin haka a aka samu a wannan majalisa mai karewa sai dai ina fatan Allah ya sa wadanda za su zo za su fahimci haka domin a ciyar da kasa gaba.
Shugaban majalisa mai barin gado, Bukola Saraki, Yakubu Dogara na majalisar Tarayya, da sugabannanin majalisar ne suka halarci wannan gayyatar bude baki da shugaban Buhari ya gayyace su.