Ma’iakatar Tsaron Najeriya ta nisanta kanta daga wani takarda da ake ta yadawa na wani kungiya da ake kira NPC da ba a san ko su waye ba suna kira da ayi juyin mulki a Kasar nan.
Mataimakin Darektan yada labarai na ma’aikatan tsaron Najeriya, Muhammed Wabi ya ce Rundunar sojojin Najeriya da ma’aikatar tsaron kasar nan na tare da gwamnati mai ci sannan kuma sai inda karfin ta ya kare wajen ganin ba a wargaza tsarin mulkin dimokradiyya da ake ciki a kasar nan ba.
Wabi ya ce takardar da kungiyar NPC ke rabawa na kira ne da akafa shugaban rikon kwarya a kasar nan a kau da Buhari daga kujeran shugaban Kasa.
” Rundunar Sojin Najeriya na nisanta kanta daga wannan takarda sannan tana so ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tana tare da wannan gwamnati da tsarin mulkin dimokradiyya da ake yi a Najeriya. Ba mu san ko su waye suke wannan kungiya da ya karade gari ba.
Kungiyar tayi kira da a taya ma’aikatar tsaro zakulo ko su waye wadannan kungiya domin hukunta su. Ya ce rundunar Sojin Najeriya ta san matsayin ta a tsarin siyasar Najeriya, ba za ta yi ayyukan gwamnati katsalandan ba.
Discussion about this post