A KULA: Tsananin ciwon kai ga mace mai ciki na kawo hawan jini – Bincike

0

Sakamakon binciken da wasu likitoci dake jami’ar Aarhus kasar Denmark, ya nuna cewa dole ne fa a rika maida hankali wajen samawa mace mai ciki dake yawan fama da matsanancin ciwon tun da wuri domin gujewa kamuw a da Hawan jini.

‘Migrane’ wani tsananin ciwon kai da kan hana mutum sukuni kwata-kwata idan ba an yi sauri-sauri bane an sama masa magani musamman mace mai ciki.

Akan kamu da irin wannan ciwon kai ne idan mutum yan a wa kansa kauran abinci, motsa jiki, rashin samun hutu yadda ya kamata damuwa da sauran su.

Alamun cutar sun hada da yawan kwarara amai, yawan ciwon kai musamman a bangare daya, zazzabi da sauran su.

Jagoran likitocin Nils Skajaa ta ce ciwon irin wannan ya fi kama matan da suke shekarun haihuwa wato daga 15 zuwa 45.

Skajaa ta ce mata kan kamu da wannan cutar ne a dalilin yawan yin fida a lokacin haihuwa, haihuwar da bakwaini, kamuwa da zazzabin dake sa arika suma, rashin cin abincin dake inganta kiwon lafiyar mace da dan dake cikinta da sauran su.

Ta ce sakamakon binciken ya nuna cewa ciwon kai irin haka na kawo cutar hawan jini ga mace mai ciki da dan dake cikinta.

Idan ba ba manta ba a kwanakin baya ne Shugaban kungiyar ma’aikatan jinyar da suka kware wajen kula da yara kanana ta Najeriya Olubunmi Lawal ta bayyana cewa Najeriya na jerin kasashen duniya uku da suka fi fama da matsalolin haihuwar bakwaini.

Bakwaini sune jariran da ake haihuwa basu wuce wata bakwai a cikin uwayen su ba ko kuma sun wuce amma basu kai watanni tara da ake zaton mace zata haihu ba.

Ta ce bincike ya nuna cewa kasar Sin itace kasar dake kan gaba wajen yawan jariran da ake haifa basukai watannin haihuwa ba sannan sai kasar India da ke bi mata. Najeriya ce ta uku cikin jerin kasashen da ake haihywar irin wadannan jarirai har 773,600 duk shekara.

Ta fadi haka ne a taron ranar Bakwaini da ake yi duk shekara inda ta kara bayyana cewa bincike ya nuna cewa akan haifi bakwaini miliyan 15 a duniya duk shekara inda kashi 60 bisa 100 daga ciki ana samun su ne a kudu da Saharan Afrika.

Dalilai 6 dake sa a haifi da bakwaini:

1 . Shan Taba Sigari

2. Mai dauke da Cutar siga (diabeties) ta Uwa ko ta uba.

3. Amfani da magungunan da wasu mata masu ciki ke yi batare da umurnin likita ba.

4. Shan giya.

5. Rashin cin abincin da ya kamata.

6. Yawan rashin samun natsuwa da kwanciyar hankali ga mai ciki.

Share.

game da Author