Kwamishinan ‘yan sandan jihar Ondo Undie Adie ya bayyana cewa sun kama mutumin da ya babbake ‘yan uwan budurwarsa saboda ta fasa soyyaya dashi a kwanankin baya.
Adie yace rundunar ta kama Deji Adenuga mai shekaru 45 ne ranar 28 ga watan Afrilu a Ijebu Ode.
” Bincike ya nuna cewa Adenuga tsohon mai laifi ne domin a 2012 Adenuga ya kashe matarsa da hakan ya sa aka daure shi a kurkukun Olokuta sannan a 2015 gwamnati ta yi masa afuwa.
Adie ya ce kotu za ta hada da tsohon da sabon laifin da Adenuga ya aikata domin hukunta shi.
Da yake hira da manema labarai Adenuga ya ce cutar sa da tsohuwar budurwarsa Titi da yayanta mai suna Jimoke suka yi ne ya sa ya aikata wannan mummunar aiki.
” A lokacin da nake tare da Titi ni ne ke ciyar da ‘ya’yan Jimoke sannan a duk lokacin da muka sami matsala da Titi Jimoke kan yi amfani da wannan dama wajen karban kudi a hannu na da sunan zata shirya mu.
” Titi ta zubar mun da cikin wata hudu duk da na roke ta kada ta aikata haka sannan ta yi sama da fadi da wasu kudade na da suka kai Naira 55,000.
” Tura ya kai bango ne a ranar da Jumoke ta yi mun barazanar cewa ni tsohon mai laifi ne wanda idan ta shigar da kara a kai na hukuma baza ta bata lokaci ba wajen kama ni saboda haka dole na ci gaba da bata kudi.”
Adenuga yace ya yi takaicin mutuwar mutane takwas a dalilin wutan da ya cinna wa gidan su Titi domin ya yi haka ne saboda kashe Titi da Jimoke kawai ba da sauran ‘yan uwanta ba.
Idan ba a manta ba a ranar 23 ga watan Afrilu ne Adenuga ya bankawa gidan budurwarsa mai suna Titi wuta saboda fasa soyyaya da ta yi da shi.
Adenuga ya aikata haka ne a cikin dare yayin da ‘yan uwan budurwarsa ke barci.
A dalilin haka kuwa mutane biyar suka mutu nan take sannan daga baya wasu uku suka karisa a asibiti.
Titi ita kadai ce ta rayu daga cikin ‘yan uwanta tara sannan tana kwance a wani asibiti a jihar Ondo.