A gaba na aka gudu da Magajin Garin Daura – Ciroman Bakan Daura

0

Ciroman Bakan Daura, Alhaji Ya’u, ya bayyana yadda masu garkuwa da mutane suka tura Magajin Garin Daura, Alhaji Musa Umar cikin mota suka tsere da shi.

Cikin wata hira da ya yi a yau Alhamis da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA), Ya’u ya shaida cewa maharan sun isa hofar gidan Magajin Gari bayan sallar Magariba, kafin sallar Isha’i.

“Ba mu taba ganin masifa irin ta yau ba. Tsakanin gida na da gidan Magajin Gari bai fi mita 30 ba.

“Tsakanin gidar Magajin Gari da gidan Mai Martaba, bai fi mita 50 ba. tsakanin gidan Magajin Gari da gidan Shugaban Kasa bai kai kilomita daya ba.

“Amma haka aka zo har kofar gidan Magajin Gari aka tafi da shi a cikin mota, har aka fita gari babu wanda ya kai dauki.

“A cikin Fijo 406 suka zo da kuma Jeep. Sun same shi a kan benci ya na zaune ya na jiran lokacin sallar Isha’i. Akwai cikin mutanen da ke tare da shi, wanda wani ya yi kokarin kama shi (da nufin hana a tafi da shi), sai suka harbe shi. Yanzu ya na asibiti.”

Ya’u Ciroman Baka ya ce sun rika yin harbi, kuma karar bindigar su “kamar taransifomar wutar lantarki ta fashe.” Inji shi.

“Bindigar da suka harba, na rantse da Allah babu wani ma’aikacin tsaro da ya ke de irin ta duk yankin Daura.

Daga nan sai Ya’u ya nuna halin damuwa cewa “abin ya wuce duk abin ka ke tsammani. Mun sa Allah gaba, mun kuma sa shugaban jami’an tsaro a gaba.”

Ciroman Baka ya ce ya na kofar gida ya ji kara, amma daidai lokacin da ya kusa karasawa kafar gidan Magajin Gari, har sun saka shi a mota.

Magajin Garin Garin Daura dan uwa ne ga Sarkin Daura, kuma ya na auren ‘yar yayar Shugaba Muhammadu Buhari.

Sannan kuma Dogarin Buhari ya na auren ‘yar sa.

Tsohon jami’in kwastan ne, kuma a yanzu babban dan kasuwa ne.

Share.

game da Author