Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta sanar da ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a gidan shakatawa dake garin Kajuru da ake kira ‘Kajuru Castle’.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Yakubu Sabo ya sanar da haka a takarda da ya raba wa manema labarai ranan Talata.
Sabo yace maharan sun sako wadannan mutane ne bayan namijin kokarin da jami’an tsaron suka yi.
Sai dai sanarwar bai ambato sunayen mutanen da aka sako ba sannan ba a fadi ko sai da aka biya diyya ba.
Idan ba a manta ba ranar 19 ga watan Afrilu ne mahara dauke da muggan makamai suka far wa gidan shakatawa dake garin Kajuru ‘Kajuru Castle’ inda suka kashe wata ‘yar kasar waje da wasu mutane uku.
Maharan sun far wa gidan shakatawa ne da karfe 11:30 na safiyar Juma’a a dai dai wasu masu yawon bude ido na shakatawa a gidan.
Bayan kashe ‘yar kasar waje da wasu mutane uku da maharan suka yi sun kuma yi garkuwa da wasu mutane uku daga wannan gida.