Abubuwan Tambaya 10 game da kafa ‘yan doka da Buhari ya amince ayi

0

Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Mohammed Adamu ya bada sanarwar cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya amince a kafa sabon tsari dakile matsalar tsaro, ta hanyar kafa ‘yandoka a cikin unguwanni da kauyuka da yankuna.

Ya bayyana haka a yau Talata a wurin Taron Kungiyar Sarakunan Gargajiya na Arewacin Najeriya.

An shirya taron ne tare da gudanar da shi a Kaduna, domin tattauna mawuyacin lamarin tabarbarewar tsaro a Arewa.

Sufeto Janar Adamu ya ce wadannan jami’an tsaro da za a kafa a cikin jama’a, za su taimaka wajen ganin an samu gagarimar nasarar tsare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma kawar da barazanar tashe-tashen hankula a cikin al’umma.

Adamu ya kara da cewa wannan sabon tsarin kawar da barazanar tsaro, zai kai ga kafa jami’an da aka fi sani da ’yandoka, wato ‘Special Constables’.

Ya ce an dauko wannan samfur din tsarin magance kalubalen tsaro ne daga tsarin ‘yan sandan Ingila.

Sannan kuma ya ce za a tsara su ta yadda za su tafi tare da tsarin jami’an tsaro na gargajiya a Arewacin Najeriya.

“Wannan tsari na ’yandoka za a dauko su ne daga cikin al’umma, kuma zai kasance aiki ne na sa kai a matsayin su na ’yan sandan cikin unguwa, jama’a ko karkara. Amma kuma za su kasance su na karkashin ’yan sanda ne.

TAMBAYOYI GOMA

1 – Shin iyakacin su farautar batagari a cikin unguwanni ko kuwa har cikin daji za su rika sintiri?

2 – Ko za a kafa dokar da za ta ba su damar rike bindigogi kamar sauran jami’an tsaro?

3 – Shin haka kawai za a bar su zaman kato-da-gora ko bulala, ko kuwa irin kulaken ’yandoka na can da za a ba su?

4 – Za a dinka musu kayan sarki ne, wato ‘uniform’, ko kuwa riguna irin na dogarai za a dinka musu?

5 – Wa zai rika biyan su albashi?

6 – Ko kuwa tunda aikin-sa-kai ne, za su yi ta yi ne ana sa musu albarka babu alawus?

7 – Yaya za a tantance nagari da kuma mugu a wajen daukar wadanda za su yi aikin ‘yandokan?

8 – Ta yaya za a sa musu ido yadda ba za su rika daukar doka a hannun su ba?

9 – Ta yaya za a bambanta su da ’yan bijilante?

10 – Ko akwai gejin karatun da ake so matashi zai yi kafin a dauke shi, ko kuwa layi matasa za su kato-bayan-kato a yi ta daukar sunayen su?

Share.

game da Author