Hukumar Gidajen Yari ta kori wani ma’aikacin ta dake shigo wa firsinoni da kwaya

0

Hukumar kula da gidajen Yari ta kasa ta ta kori daya daga cikin ma’aikatanta da aka kama da aikata laifin safarar miyagun kwayoyin wa firsinoni.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Francis Enorbore ya sanar da haka ranan Litini a Abuja.

Enorbore ya ce hukumar ta kori ‘Prison Assistant 1’ Umar Adamu bayan kwamitin hukunta masu aikata laifuka na ‘Zone C’ ta gudanar da bincike akan laifin da ake zargin sa da shi kuma an kama shi da aikata haka.

Sakamakon binciken ya tabbatar cewa Adamu na safaran miyagun kwayoyi da suka hada da tabar wiwi da sauran su wa mazaunan gidan yari.

Enorbore yace daukan wannan matakin na cikin matakan da NPS ta dauka domin kawar da miyagun aiyukkan da wasu baragurbin ma’aikata ke yi a gidajen yarin kasar nan.

Enorbore yace daga yanzu shugaban hukumar yace a kori duk ma’aikacin da aka kama da laifin aikata haka a hukumar sannan ya tabbatar wa mutane cewa hukumar za ta ci gaba da aiyukkan ta na kawar da masu aikata miyagun aiyuka.

Share.

game da Author