Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya san irin tuggun da za abi a kawo karshen Uban-gida a siyasar jihar Legas.
El-Rufai ya fadi haka ne a wani taro da ya halarta ranar Asabar a Legas.
El-Rufai yace shine ya yayi wa wasu ‘yan siyasa a Kaduna da suka rike wa mutanen jihar makogoro, ‘Yan siyasan da ake cewa idan basu tare da kai ba zaka kai labari ba a siyasar Kaduna aba.
“ Tuni na yi awon gaba da su yanzu sun zama tarihi a jihar Kaduna. Sannan ku fa sani maganan iyayen gida duk a baki yake ko kuma a rubuce amma basu da wani tasiri.
“ Akwai wasu mutane uku ko kuma in ce hudu da duk abinda kake so ka nema a siyasance a Kaduna sai ka bi su sau da kafa ka yi musu bauta sannan ka samu. Bautar kuwa shine ka rika narka musu kudi kawai.
“ Da muka zo sai muka ki bin wannan hanya ta su, muka yi watsi da su mu ka canja salon mulki. Yanzu.
El-Rufai yace idan ana so a kau da matsalar iyayen gida ko kuma uban-gida, toh dole sai sai ‘yan siyasa sun koma ga talakawa.
Sanin kowa ne cewa tun bayan zaman sa gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ya zama shine wuka shine nama a siyasar jihar. Shine yake nada duk wanda zai zama gwamna a jihar.
Idan ana so a kau da Tinubu a jihar Legas El-Rufai yace dole ne, na farko dai mutum ya tanaji naira biliyan 2 a kasa sannan mutum ya fara bin diddigin sanin dalilin da ya sa miliyoyin mutane basu yin zabe a jihar legas. Wadannan zai bi ya rika dadadawa rai har sai sun yi na’am da shi.
Sai dai kuma yace hakan na bukatan makudan kudi da ya kai akalla naira biliyan 2.
Da zaran ka yi haka toh, komai zai zo da sauki. Amma fa El-Rufai yace duk masu shirin haka sai su faro tun yanzu domin yana daukar lokaci sosai.
“ A Kaduna mun yi musu ritaya har da wanda yake cewa wai shine ya dora ni kan kujerar gwamna kuma shine zai wancakalar da shi.