Sama da kananan yara 3,500 Boko Haram suka maida mahara a Arewa maso Gabas -UNICEF

0

Asusun Tallafawa Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF), ta hakkake cewa akwai yara sama 3,500 ne ‘yan bindiga suka tilasta yin yakin sari-ka-noke a Arewa maso Gabas cikin Najeriya.

UNICEF ta ce an rika tilasta horas da su tare da koya musu atisayen kai hare-hare tun daga 2013, kamar yadda ta jaddada.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yaran wadanda akasari sun kama daga shekaru 13 zuwa 17, an horas da su ne tsakanin 2013 zuwa 2017, kuma da su ake ta gumurzun yake-yake da hare-haren da ake yi a Arewa maso Gabas.

Haka dai UNICEF ta bayyana a yau Juma’a da safe, ta hannun daya daga cikin manyan jami’an ta, mai suna Eva Hinds.

Yayin da suke jimamin ranar cikar kama daliban Chibok shekaru biyar, wato tun 2014, Majalisar Dinkin Duniya tahannun UNICEF, ta ce wadannan adadin yara 3,500, ba kirdado ko kintace ba ne, bincike ya tabbatar da an horas da su din. UNICEF ta ce zai iya yiwuwa ma adadin ya haura haka.

Baya ga wadanda aka horas, UNICEF ta kara da cewa a cikin 2018 kadai an karkashe kananan yara har 432, an sace 180, sannan kuma an yi wa kananan yara mata 43 fyade, duk a Arewa maso Gabas.

Sannan kuma UNICEF ta ce har yau ba a daina tilasta wa mata auren wadanda suka sace su ba, tun daga 2012 har zuwa yau.

Akwai kuma matsalar wadanda ake sacewa, ana dirka masu ciki, su na haihuwa inda babu jami’an kula da majiyyaci ko nas-nas.

“Cikin 2017 da 2018, UNICEF da wasu kungiyoyin bincike sun tabbatar da cewa sun gudanar da ayyuka ga mutane sama da 9,800 wadanda a baya sun yi mu’amala da ‘yan ta’adda.”

UN ta kara da cewa ayyukan da ta ke gabatarwa din sun taimaka wajen zakulo iyayen yaran, suka maida su wajen iyayen na su, sannan kuma suka yi musu agajin taimako a bangaren ilmi, horon koyon sana’o’in hannu da sauran hanyoyin samun damar inganta rayuwar su.

Wakilin UNICEF, Mohammed Malick ya ce aka daliban Chibok da aka yi, sannan ake rike da sama da 100 daga cikin su, ya nuna cewa har yanzu ana ci gaba da samamen kamen kananan yara ta hanyar sace su da tauye musu hakkin su a yankin Arewa maso Gabas.

Ya kuma yi kiran da a gaggauta kawo karshen wadannan fadace-fadace.

Share.

game da Author