Hausawa sun ce: ‘Tsuntsun da ya kira ruwa, shi ruwa ke wa duka.”
Wannan karin magana ta faru ga dan wasan Atletico Madrid, Diego Costa, wanda cikin wannan makon ne Hukumar Kwallon La Liga ta kasar Spain ta dakatar da shi buga wasanni har 8 a jere.
Wannan ya biyo bayan buyagin da Diego Costa ya yi wa alkalin wasa, Gil Manzano, a wasan da Atletico ta yi rashin nasara a hannun Barcelona, ranar 6 Ga Afrilu.
Tun a daidai minti na 28 aka daga wa Costa jan kati, bayan da ya cakumi damtsen alkalin wasa ya nemi hana shi dauko kati daga aljihu.
Costa ya hakikice cewa shi ne aka yi wa keta, na shi ne ya yi ketar ba. Wannan bai hana a daga masa Jan kati ba, wanda shi kuma Costa ya ce ba zai fice daga filin ba.
An yi hatsaniyar da sai da ta kai dan wasan Barcelona, Gerard Pique ya je ya ba shi hakuri, sannan ya kama hannun sa ya nufi wajen fili da shi.
Kwamitin Ladabtar Da ‘Yan Wasa ya zauna shekaranjiya Laraba, inda aka yanke wa Costa hukuncin hana shi buga wasanni 8 a jere.
Hakan kenan na nufin ba zai kara buga was an La Liga ba, sai wata kakar wasan kenan. Tunda wasannin da su ka rage ba su kai goma ba.
A na sa bangaren, alkalin wasa ya rubuta rahoton korafi cewa Costa ya cukumar masa damtsen hannu, kuma ya surfa masa ashar.
“Ya zunduma wa mahaifiya ta zagi, ya ce min: ” Na tula kashi a fuskar uwar ka, karuwar nan!” Inji alkalin wasa Manzano.
Costa dai bai ji dadin kakar wasan bana ba, domin a cikin wasanni 21 da ya buga, kwallo biyar kadai ya ci. Daga cikin 5 din, guda biyu kadai ya ci a gasar La Liga.