A ranar Juma’a ce dubun wani tsohon shuagaban karamar hukumar Kafin Hausa dake Jihar Jigawa, Aliko Kwatalo a daidai ya na kwance da natar makwabcinsa a gidan makwabcin.
Wannan abin tashin hankali da ban haushi ya auku ne a rukunin gudaje na NTA dake titin Garin Gabas a karamar hukumar Hadeja.
Mijin wannan mata Fatima, mai suna Danliti Abubakar ne ya kawo kara ofishin ‘yan sanda bayan ya kama su da kan sa.
” A wannan rana na shirya zan fita daga gida sai na ji matata tana waya a boye. Sai na kasa kunni naji tana fadin ga yadda zasu hadu da kwarton nata.
” Dana ji haka sai ban ce mata komai ba. Na lallaba kamar na fice zuwa wajen aiki. Muka yi sallama.
Bayan dan wani lokaci sai ga makwabcina Malam Kwatalo ya lallabo ya shigo gidana.
Abubakar yace sai da ya bari Malam Kwatalo ya dan dauki lokaci kadan a cikin dakin matar sa sai ya lallaba ya kulke kofar ta waje. Sannan ya yi maza maza ya kira Hisbah,’yan sanda da sauran mutanen unguwa.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Audu Jinjiri ya tabbatar da aukuwar haka.
Jinjiri ya ce rundunar za ta gabatar da Malam Kwatalo da matar Abubakar,Fatima Usman mai shekaru 25 a kotu.