Antony Janar kuma Minstan Shari’a, Abubakar Malami, ya nemi Hukumar Ladabta Ma’aikata (ICPC), ta damka masa fayil din da ke kunshe da tuhumomin da ake wa Shugaban Hukumar Kula Gidajen Radiyo da Talbijin, Modibbo Kawu.
ICPC ce ta maka Kawu a kotu, inda ake tuhumar sa da yi wa naira bilyan 2.5 kisan sabon-kama-kudi.
Wannan harkalla dai ta kawo tsaiko wajen kokarin da Gwamnatin Tarayya ta yi sauya tsarin kamo tashoshin talbijin daga na game gari tsohon yayi, zuwa na zamani, wato ‘digital transmission.’
An gurfanar da Kawu a kotu tare da wasu shugabannin wani kamfani mai suna Pinnacle Communications Limited.
Jami’an kamfanin sun hada da Lucky Omoluwa, Dipo Onifade da kuma shi kan sa kamfanin na su, wato Pinnacle.
‘KATSALANDAN’ DAGA MINISTA MALAMI
Kwanan nan katsam sai PREMIUM TIMES ta samu tabbacin cewa a ranar 26 Ga Maris, Malami ya rubuta wasika ya na neman a aika masa fayil din bayanan tuhume-tuhumen da ake yi wa su Modibbo da kamfanin Pinnacle, domin ya yi nazarin kwakwaf.
A dokar Najeriya, Antoni Janar, wato Ministan Shari’a na da ikon da zai nemi gani ko yin nazarin kowace shari’a da Gwamnatin Tarayya ta maka wani a kotu, matsawar karar ta shafi tabka laifi.
To amma kuma PREMIUM TIMES ta gano cewa jami’an hana harkalla, karma-karma da sama-da-fadi da kudaden gwamnati sun fusata da abin da suke ganin cewa wani yunkuri ne Malami ke kokarin yi domin ya karya lagon wata babbar harkalla.
An ce su kuma sun ci maganin kin amincewa su damka masa fayil din.
Sannan kuma sun jefa alamar tambaya ga daidai lokacin da Malami ya nemi a bas hi fayil din.
A gobe Laraba ne dai za a gurfanar da Kanu a kotu, bayan ya sha kin halarta a baya, a bisa dalilin sa na rashin lafiyar da ya ce an kwantar da shi asibiti.
A zaman karshe a aka yi ne a kotu, cikin watan Maris, Mai Shari’a ta ce a kai mata Kawu a ranar 17 Ga Afrilu, ko da a kan gadon asibiti ya ke, to a tattago shi a kai mata shi.
Gurfanar da Kawu da za a yi gobe Laraba, ya nuna cewa ICPC ta bijire wa umarnin Abubakar Malami kenan.
Ba wannan ne karon farko da Malami ya tsoma hannu da kafafu a cikin sha’anin wasu shari’un wasu manya a kasar nan ba.
Ya yi a wata shari’a da ke gaban wata kotu a Katsina, kuma ya yi wa gagarimar shari’ar nan ta Malabu Oil, wadda ake kan tabkawa ta zargin wuru-wurun dala bilyan 1.3
Jami’an EFCC sun ki amincewa da shawarar sa a kan shari’ar Malabu, inda suka bijire wa umarnin sa, suka ci gaba da maka wadanda ake tuhuma a kotu.
PREMIUM TIMES ta zauna da Modibbo Kawu, inda a hirar da ta yi da shi, ya wanke kan sa daga dukkan zarge-zargen da ake yin masa.
Ya musanta cewa ya yi wata harkalla, sama-da-fadi ko kashe-mu-raba da kamfanin Pinnacle Communications Limited, duk kuwa da cewa mai kamfanin abokin sa ne, a tsawon shekaru 30 su na tare.