Na jima a cikin damuwa da tunani marasa adadi a ranar da nayi tozali da kalaman Ministan tsaron Najeriya General Mansur Dan Ali a fuskokin manyan jaridun kasa da kuma kafofin sa da zumunta na zamani, inda yake zargin Sarakuna su ne kan daurewa ‘yan ta’adda gindi wajen aikata miyagun ayyuka kususan a Arewa, kuma yankunan Zamfara da har yanzu ake fama da kalubalen tsaro.
Kalmar “ministan tsaro” da kuma “sarakuna” su ne ababen daukar hankalin ba wai wadanda ke rike da mukaman ba. Domin kai tsaye wannan zargi zai iya zamowa wani babban cikas ko kafar ungulu wajen bayar da hadin kai daga su sarakunan don ganin an dakile wannan matsala da ake ta fama da ita.

Mutumin da yake Karkara idan irin wannan bayanai suka shiga kunnuwansa, to kai tsaye zai shiga rudani da rashin tabbas. Domin kafin ya nutsu ya tantance abin da ministan ya ke nufi(idan ma akwai gaskiya a ciki) to barnar da kalaman za su yi a cikin gari, ba karami ba ne. A hankali kananan maganganu za su fara yawo suna zagawa a kauyuka, kuma daga lokacin ne idan ma akwai wata a kasa tsakanin mutanen da ake mulka, da sarakunan, sai a fara samun matsaloli. Har a wasu lokacin wasu suna ikirarin ai manyansu ake bawa kudi ana kashesu kamar kaji.
Wani lamari da ya zamar mana matsala ko cuta a Arewa, musamman a fannin zamantakewarmu shine, idan abu ya faru, ba ma zama mu kira mutane ma’abota sani a bangarori da dama na rayuwa su nazarci wata matsala da ta kunno kai, a karshe su futar da bayanai na hankali, wanda da su za ayi amfani a gabatarwa hukuma, da kuma sauran al’umma don ganin an samu mafuta da sauki, gami da faruwar irin wannan matsala a gaba. Amma sai dai mu na ta kame-kame da zargin juna, a karshe sai siyasa da addini su samu gurbi, shikenan kuma sai abin da hali yayi. Sai abubuwa sun gama cushewa sai kuma a koma wajen malamai da sarakuna ana cewa su fara addu’a tare da yi wa mutane tsawa da sauransu. Kuma wannan tsari an barshi tun karni na wajen sha takwas.
Mudi Spikin ya taba cewa “Kwarkwata, Tsiya, Talauci da Ha’inci, duk Jahilci ke kawo su” Kun ga kenan rashin ilimi a dunkule zai iya jefa al’umma cikin kowanne irin tashin hankali da garari a rayuwa. Kuma madamar ba a kawo tsarin ilmantar da al’umma musamman mata ba, to ba shakka za mu sha mamaki nan da wasu shekaru hamsin masu zuwa.
Bari na bayar da misali, a lokacin da Boko Haram suka fara kaddamar da babban hari a watan Yuli na shekarar 2009 a garuruwan su Wudil da wasu yankuna a Borno, ai wasu mutanen har tafi suke ana shewa, wai jami’yan tsaro da gwamnati ake kai wa hari. Kuma duk mutum mai ilimi da ya san kansa da kishin kasa, hawaye zai zubar ba murna ba. Yau gashi ana bikin cika shekaru biyar da kame ‘yan matan Chibok da Boko Haram din suka yi garkuwa da su. Abubuwa marasa dadi ya faru akan su da kuma na kusa da su. Kuma har daren gobe Boko Haram za ta ci gaba da zama kakubale idan har ba ayi wani tsari mai ma’ana ba.
Ina so na tambayeka mai karatu, a wane lokaci da zarar matsala ta taso a Arewa ko wasu yankunanmu, nan da nan manyan malamai da sarakuna da ‘yan boko gami da ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa da wani sashi na dalibai da matasa masu hankali, ake kiran taron gaggawa domin a nazarci wannan matsala da ta kunno kai, gami da yin kandagarki, da kuma dusasar da kaifinta?
A yau, akwai jihohi kusan bakwai a Arewa masu yamma, kuma yanki mafi karfi a Najeriya. Don sarkin musulmi da shugaban kasa gami da attajirin Afrika, duk anan suke, wannan idan ka dauke manyan malaman addini ne da ‘yan boko gami da manyan jami’yan tsaro, amma yaushe aka taba haduwa ko a sirri ne don ganin an yi wa yankin wani tsari na shekaru kamar ashirin masu zuwa da zai kawo mana saukin halin da muke ciki?
Kwanaki Sanata Kabir Marafa ya kai kuduri majalissa, har ma an amince za a bawa jihar Zamfara biliyan goma don kawo saukin barnar da asarar rayukan da aka yi. Idan har burinmu sai matsala ta samemu za mu je a bamu kudi, manyanmu su cinye, al’umma na cikin tashin hankali, to zamanmu a duniya ma bashi da amfani. Domin a cikin bautawa mahalicci akwai kare hakkin jini da kyautatawa halittu, kasancewar don bautar aka haliccemu.
Idan har burinmu mu ma a kafa mana North West Development Commssion kamar yanda aka kafa a Arewa maso gabas da Kudu maso Kudu, to a gaskiya mun yi asara mun lalace a matsayinmu na al’ummar daular Usmaniyya.
Daga karshe, ina kira ga junanmu baki daya, mu yi hakuri mu saba da kokarin fadawa juna gaskiya. Mu mike tsaye mu fahimci me yake damunmu. Mu hada kai, mu taimakawa al’umma. Mu bayar da ilimi da samar da aikin yi ga matasa, gami da kira ga malamai su dukufa waje yin wa’azi na amana ba na cin nama ba, don ganin an samu al’umma ta gari a nan gaba. Dole ne jagorori da shugabanni su hada kai su tunkari duk wata matsala da ta kunno mana kai, ba tare da waiwayen bangaren addini, siyasa ko asalin sarautar Habe ko Sullubanci ba. Ta hakane kadai nan da wasu shekaru mu ma za mu zama abin sha’awa da kwarjini ga sauran kasashen duniya, ba ma wadanda muke tare da su a nan Najeriya ba!