Duk da rashin tsaro da kashe-kashen rayuka da ake fama da shi a jihar Zamfara, jam’iyyu 43 na nan na shirin fafatawa a zaben kananan hukumomin da za ayi a jihar.
Hukumar zabe ta jihar ta tsayar da ranar 27 ga watan Afrilu a matsayin ranar da za a yi zaben kananan hukumomi a jihar.
Jami’in hukumar na jihar Bello Wadata ya sanar da haka da yake zantawa da Kamfanin Daillancin Labaran Najeriya ranan Litini.
Wadata ya ce hukumar ta zauna da masu ruwa da tsaki a jihar domin tattaunan yadda za a tunkari zaben.
Wadata ya ce suna sa ran cewa shiri da matakai da hukumar ta dauka game da zabe zai taimaka wajen ganin zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali.