GOSA KPANYI KPANYI: Gari kusa da Abuja, amma ba wuta, ba ruwa

0

Mazauna garin Gosa Kpanyi Kpanyi da ke cikin Karamar Hukumar Kuje, sun koka dangane da matsanacin kuncin rayuwa da suke fama da shi a garin, duk kuwa da cewa su na karkashin Yankin Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Babbar matsalar su ita ce rashin ruwan sha, rashin hasken lantarki sannan da kuma rashin kayan more rayuwa a matsayin su na mutane, kuma makusanta FCT.

Da yawan wadanda aka zanta da su, sun bayyana cewa kusan shekara 40 su dai babu wani abu da gwamnati ta tsinana musu, da za a iya cewa gwamnati ta san da zaman su.

Gosa Kpanyi Kpanyi dai ya na kan hanyar Filin Jirgin Abuja, kuma akwai haskenn lartarki na fitilun kan titi da suka bi ta daidai gefen shiga garin. Amma fa cikin garin ko rami bai fi shi duhu ba.

Wani dan garin mai suna Tanko Joshua, ya bayyana cewa tun da aka haife shi a garin har girman sa, babu wani abin more rayuwa guda daya da gwamnati ta taba yi musu da har zai tabbatar da cewa gwamnati ta san da su, kuma ta na kulawa da su.

“A Gosa aka haife ni, a nan na tashi, amma ni dai daga shekaru 40 da suka gabata har zuwa yau, ban ga hasken lantarki a Gosa ba.

“Akwai shagon wani mutum da mu ke zuwa kowa ya na cajin wayar sa ko filita. Ya na cajin kowa naira 50 a duk waya guda daya ko fitila daya.

“Ga dai turakun wutar lantarki nan ka na gani an kafa mana tuni. Amma amma ko fal-waya ba a sake dawowa an daura ba, ballantana mu yi tunanin samun wutar lantarki kuma.

“Babu makaranta a Gosa Kpanyi Kpanyi. Tilas sai ‘ya’yan mu sun tsallaka sun tafi garin Gosa Seriki idan za su yi karatu, domin a can makanta ta ke.”

Shi kuwa Bako Haruna, ya na Babbar Sakandare ne, ya na jin haushin yadda ‘yan siyasa ke yawan rige-rigen zuwa garin kamfen, tare da yi musu alkawarin ababen more rayuwa. Amma dukkan su duk wanda ya ci zabe ba ya kara waiwayar su, ballantana ma ya cika alkwarin da ya dauka.

Wata mata mazauniyar Gosa Kpanyi Kpanyi, ta ce ba za ta ambaci sunan ta ba, amma kuma ta tabbatar da cewa shekarar ta 20 a cikin Gosa, amma ba ta taba ganin an kyallo musu ko da harken lantarki na sakan daya ba.

“Ba mu da asibiti, babu makaranta, babu ruwan sha, babu hasken lantarki. Idan mace na da tsohon ciki, to sai dai ta je asibitin Lugbe ta haihu.

“Gosa kadai ne garin da ke kan titin zuwa Filin Jirgin Abuja da ba shi da hasken lantarki da sauran ababen more rayuwa. Ga mu da wuta a bakin titi, amma babu a cikin garin mu.

Shi ma wani mai suna Danjuma Musa, ya shaida cewa shekara biyu baya kamfanin samar da wutar lantarki na Abuja, wato AEDC, ya kafa turakun wuta a garin, amma har yau bai sake waiwayar su ba.

“Ai mun gane ashe dama abin yaudara ce kawai, saboda a lokacin an ga zabe ya gabato.” Inji Danjuma Musa.

“Wancan kogin da ka ke gani wanda ake tsallakowa idan za a shigo garin nan, shi ne mashayar ruwan mu.”

Ita ma wata mai suna Endurance Ephraim, cewa ta yi shekarar ta 20 cikin Gosa Kpanyi Kpanyi, amma ba a taba kafa musu ko da kan famfon ruwa guda daya ba.

“Ruwan da mu ke amfanin yau da kullum, ba shi da tsafta, domin akwai abubuwa masu barazana ga lafiya a cikin kogin na Wupa. Akwai kuma duwatsu masu kaifi a ciki.

Ta ce amma tilas su na ji su na gani ba don sun so ba, yaran su za su rika tafiya cikin rafin su na wanka, saboda tsananin zafin da ake kwamtsawa.

“A baya har shan ruwan muke yi, amma sai muka lura da yaran mu sun rika fama da tsargiya, wato fitsarin jini. Sai muka daina shan ruwan, amma dai har yanzu mu na yin amfanin yau da kullum da ruwan.

“Za mu dai je mu yi wanka, mu yi wankin tufafi, sannan kuma shanu da tumakai ma za su je su sha, su kuma yaran mu su yi wasan kurmuye a cikin ruwan. Idan ruwan ya shiga jikin su kuma su yi ta fama da fitsarin jini.” Inji ta.

Share.

game da Author