Kamfanonin Samar da Karfin Hasken Lantarki, wadanda aka rada wa suna GenCos, sun fitar da sanarwar cewa sun saki wuta mai karfin migawats 3,522 a ranar 7 Ga Afrilu.
Sun yi wannan bayanin a wani rahoton da suke fitarwa a kowace rana, wanda suka fitar yau Litinin da safe.
GenCos sun ce wutar da suka saki ta kunshi wadda suka saki daga tashoshin raba wuta masu amfani da gas da kuma tashoshin da ake tatsar wuta ta hanyar amfani da madatsun ruwa.
Sun ce karfin wutar ya ragu da migawats 657.07 daga wadda aka saki kuma aka rarraba a ranar Asabar da ta gabata.
GenCos sun ce sun kasa rarraba migawats 1,771 da ya kamata su rarraba, saboda matsalar rashin gas da za a yi amfani da shi wajen kunna injinan rarraba wutar.
Akwai wata migawats 202.70 da ita ma aka kasa rarrabawa saboda rashin karfin kayan aikin sarrafa karfin makamashin lantarkin.
Kenan an kasa raba wasu migawatas 2,369.30 saboda matsalar kayan sarrafa makamashin nhasken lantarki har a rarraba shi.
Sun ce akalla sun yi asarar naira biliyan 2.1 a ranar Lahadin jiya, saboda matsalar rashin wadataccen gas da za su iya aikin rarraba karfin wuta da shi.
GenCos sun ce amma duk da haka, can tsakar dare an samu raba karfinn wutar da ta kai migawats 4,190 a ranar, a fadin kasar nan baki daya.