RANAR KIWON LAFIYA: Najeriya za ta bunkasa shirin Inshorar kiwon lafiya ta kasa – Minista

0

Ranar kiwon lafiya ta duniya:WHO da gwamnatin tarayya sun hada hannu domin samar da ingataccen lafiya ga kowa da kowa.

A ranar kiwon lafiya ta duniya ne Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa za ta ci gaba da mara wa gwamnatin Najeriya baya domin samar wa mutanen kasar kiwon lafiya mai nagarta kowa da kowa.

Jami’in WHO Rex Mpazange ya sanar da haka a taron bukin zagayowar ranar Kiwon Lafiya ta Duniya.

Ya ce kungiyar WHO za ta mara wa fannin kiwon lafiyar Najeriya ne ganin irin namijin kokarin da take yi domin inganta fannin da kuma amincewa da ware wa fannin akalla kashi daya daga cikin kasafin kudin ta na duk shekara.

Mpazange ya kuma yaba wa gwamnati bisa shirin inshoran kiwon lafiya da ta kirkiro domin samarwa mutanen kasar kiwon lafiya cikin sauki.

” Wadannan dabaru da gwamnati ta dauka na cikin dabarun da za su taimaka mata wajen cin ma burinta na samar da kiwon lafiya mai nagarta ga kowa a kasar.

Sai dai kuma duk da wannan yabo da aka rika kwarara wa Najeriya babban darektan kungiyar WHO Tedros Ghebreyesus kira yayi ga gwamnatin kan karfafa ayyukan cibiyoyin kiwon lafiya a kasar domin dakike yaduwar cututtuka a kasar.

Ghebreyesus inganta cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko shine tsarin da yafi dacewa domin samun ci gaba a fannin kiwon lafiyar kasarnan.

A nashi jawabin ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa gwamnati ta zage damtse matuka domin inganta asibitocin kasar nan don rage yawan fice wa daga kasar domin zuwa wasu kasashe neman magani.

” Bincike ya nuna cewa mutanen kasar nan kan fita zuwa kasashen waje neman magani musamman ga cututtuka da suka hada da cutar koda, cututtukan dake kama zuciya da daji da sauran su.

” Mun saka kayan aiki a asibitocin dake jihohin Sokoto,Edo da Enugu sannan gwamnati na kokarin kafa tsarin da zai taimaka wa duk asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko samun kudaden da suke bukata zuwa aljuhan su kai tsaye ba tare da wani shamaki ba.

A karshe ya ce gwamnati za ta karfara tsarin inshorar kiwon lafiya domin tabbatar da ganin mutanen Najeriya

Share.

game da Author