Ritaya Babban Cif Joji ya yi, ba murabus ba –Lauyan sa

0

Lauyan Tsohon Babban Cif Jojin Najeriya wanda aka dakatar watanni biyu baya, ya ce Walter Onnoghen ritaya ya yi don kan sa, ba murabus, wato ba sauke shi aka yi ko tilasta shi ya ajiye aiki aka yi ba.

Lauya Adegboyega Awomolo, wanda shi ne babban lauya kuma jagoran lauyoyin da ke kare Onnoghen a shari’ar da ake tuhumar sa da laifin kin bayyana hakikanin kadarorin da ya mallaka, ya yi wannan karin hasken ne ga PREMIUM TIMES da yammacin jiya Juma’a.

Lauyan ya ce Onnoghen ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari wasikar sanarwar ajiye aiki da kan sa, amma ba murabus ya yi ko aka yi masa ba.

Ya kara da cewa kuma a dokance ma haka ya kamata ya yi, wato aika wa Shugaba Buhari wasika kai tsaye.

“Har yanzu ya na nan a kan matsayin sa cewa Hukumar NJC ce kadai za ta iya ladabtar da shi, to yanzu tunda NJC din ta yi magana, shi ya sa ya yanke shawarar gara kawai ya nuna dattako ya sauka don kan sa. Amma ba sallamar sa aka yi ba.”

SALSALAR RIKICIN WALTER ONNOGHEN

Onnoghen ya yi ritaya kwanaki 51 bayan an fara tabka shari’ar da aka tuhumar sa da kin bayyana kadarorin da ya mallaka, a ranar 28 Ga Janairu, kwanaki 58 bayan an rubuta takardr korafi a kan sa.

An nada Onnoghen daya daga cikin Manyan Alkalan Kotu Koli a cikin 2005, sai a ranar 6 Ga Oktoba, 2016 ne aka nada shi Babban Cif Jojin Najeriya, a lokacin da Hukumar NJC ta na karkashin Moahmood Mohammed.

Sai dai kuma bai samu Majalisar Dattawa ta tantance amincewa da shi ba, sai a ranar 7 Ga Maris, 20117.

Hakan kuwa ya fru ne saboda Shugaba Muhammadu Buhari ya tsaya jan-kafa wajen aikawa da sunan na sa Majalisar domin amincewa da nadin sa.

An rantsar da shi a ranar 7 Ga Maris, 2017, inda Mukaddashin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ne ya rantsar da shi.

YADDA AKA DATSE WA’ADIN ONNOGHE
Da ya ke ranar 22 Ga Disamba, 1950 aka haifi Onnoghen, hakan na nufin sai a rannar 22 Ga Disamba, 2020 ne zai cika shekaru 70 kenan.

Tunda shekaru 70 wa’adin ma’aikacin gwamnati kafin ya yi ritaya, a ranar ce ya kamata a cewa Onnoghen ya yi ritaya daga aikin gwamnati.

Sai dai kuma an datse masa wa’adin zama kan shugabancin Manya da Kananan Alkalan Najeriya, a ranar 25 Ga Janairu, awa 24 kafin ya rantsar da Alkalan da za su yi shari’un kararrakin zaben 2019.

A lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari zai dakatar da Onnoghen, sai da ya karanto hujja daga CCT, wato Kotun Ladabtar da Ma’aikata.

An fara shari’ar Onnoghen, amma ya ki halarta, har sai da Mai Shari’a Danladi Umar na CCT ya aika wa jami’an ‘yan sanda sammacin kama shi idan ya sake kin bin umarnin kotu ya ki halartar shari’ar sa.

Ana yi masa tuhume-tuhume har guda shida, duk wadanda ke da nasaba da kin bayyana kadarorin sa.

Hukumar Ladabta Ma’aikata, wato CCB ce ta gurfanar da Onnoghen a Kotun Ladabta Ma’aikata, wato CCT.

Lauyoyi da dama sun yi tir da dakatar da Onnoghen da Buhari ya yi da kan sa. Bisa hujjar su cewa Hukumar NJC ce da kuma amincewar kashi biyu bisa uku na Majalisar Dattawa kadai ke da ikon dakatar da shi ko korar sa.

Su kuma wadanda suka goyi bayan dakatar da shi, sun nuna cewa an kafa hukumar CCB da kotun CCT, musamman dama saboda irin abin da aka yi zargin Onnoghen ya aikata.

Don haka inji su, daidai ne idan Shugaba Buhari ya dakatar da shi, kuma an gurfanar da shi a kotun.

Har ma Sashe na 308 Na Kundin Dokokin Najeriya suka kafa hujja da shi.

Ritayar da Onnoghen ya yi, za ta tabbatar da tantancewa da amincewa da Babban Cif Joji Mai Riko Mohammed Tanko a matsayin cikakken Cif Joji kenan.

Share.

game da Author