SABON HARI: Yadda ’Yan Bindiga Suka Halaka Mutane 50 A Zamfara

0

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Sanusi Rikiji, ya bayyana cewa a ranar Talata mahara sun kashe sama da mutane 50.

Rikiji ya ce akasarin wadanda aka kashe duk ’yan sintiri ne na CJTF da kuma sauran jama’a.

Haka Rikiji ya bayyana a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga Masarautar Kaura Namoda.

Ya ce wannan mummunar asarar rayuka da yawa ta faru ne sanadiyyar gangancin da ‘yan sintirin suka yi ne, inda suka dauki gaban-gabarar yin fito-na-fito da ’yan bindigar.

Kisan ya farun ne a cikin Karamar Mukumar Kaura Namoda, a Jihar Zamfara.
Kakakin, wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin jiha zuwa ta’aziyya, ya nuna matukar damuwa da irin munin da matsalar tsaro ta yi a Zamafara.

“An shaida mana cewa su ‘yan sintiri na CJTF sun hada gangamin jama’a daga kauyen Sakajiki cikin Karamar Hukumar Kaura Namoda, suka je suka tarbi mahara a cikin jeji. Wannan ne ya yi sanadiyyar kashe sama da 50 daga cikin su. Har da ‘yan sintirin CJTF da dama.”Inji Rikiji.

Ya ci gaba da jan hankali cewa babu ruwan ‘yan sintiri da tunkarar ‘yan bindiga, domin ba su kware kuma ba su gogu da yaki ba.

“Aikin da kawai aka ba su umarnin su rika yi, su rika yin sintiri, idan sun samu rahoton batagari, sai su gaggauta sanar da jami’ann tsaro. Aikin jami’an tsaro ne su tsara yadda za su tunkari ‘yan bindiga, amma ba ‘yan CJTF ne za su yi gangancin afkawa daji farautar ‘yan bindiga ba.”

Daga nan sai ya roko ki sarakunan gargajiya da su rika jan kunnen ‘yan sintiri su guji daukar doka a hannun su.

Ya ce sun kuma karbi adadin sunayen wadanda suka rasa rayukan su da wadanda aka ji wa rauni, domin a san yadda gwamnati za ta gaggauta taimaka musu.

Mai Martaba Sarkin Kaura Namoda, Muhammadu Asha, ya gode wa Gwamnatin Zamfara a bisa okarin da ta ke yi wajen ganin an dakile mahara a jihar.

A na sa bangare, Sarki Asha ya ce ya sanar da limaman masallatan Juma’ar masarautar sa gaba daya cewa ranar Juma’a a yi addu’o’i na musamman, domin rokon Allah ya magance wannan bala’i.

Share.

game da Author