Kananan yara 100,000 ke mutuwa duk shekara a dalilin rikice-rikice – Bincke

0

Gidauniyar ‘Save The Child’ ta bayyana cewa an rasa yara 550,000 zuwa 870,000 a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2017 a dalilin rikice-rikicen da ake fama da su a wasu kasashen Afrika 10.

Wadannan kasashe kuwa sun hada da Afghanistan, Yemen, South Sudan, jamhuriyan tsakiyar Afrika,jamhuriyan kasar Congo (DRC), Syria, Iraq, Mali, Nigeriya da Somalia.

Gidauniyar ta gano haka ne a bincike da ta yi sannan ta gabatar da sakamakon binciken a taron cika shekaru 100 da kafa gidauniyar da aka yi a Abuja ranar Alhamis.

Kamar yadda jami’an gidauniyar Helle Thorning ta bayyana, binciken ya nuna cewa a dalilin haka akan rasa yara kanana 100,000 a duk shekara a dalilin haka.

Wadannan illoli sun hada da yunwa, rashin asibitoci,rashin samun ababen more rayuwa,rashin zama a tsaftattacen muhali da sauran su.

Thorning-Schmidt ta ce a dalilin haka ya zama dole a hada hannu gaba daya domin kare manyan goben kowace al’uma a wadannan kasashen daga wannan matsala.

Wasu jami’an gidauniyar Wilfred Okanda da Amanuel Mamo sun yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki na wadannan kasashen kan hada hannu da gidauniyar su da sauran kungiyoyin bada tallafi domin ganin an samarwa yaran dake zama a kasashen dake fama da rikice-rikice mafita.

Share.

game da Author