A bidiyo da ya karade shafunar sadarwa na yanar gizo a yau Laraba, an ga shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Abbas yana ingiza wasu matasa da su kwana da shirin ko ta kwana a zaben da za a yi a Kano ranar 23 ga wanat Maris.
Abdullahi, zaune a kan kujera ana yi masa kirari, yace “ Sai dai bamu sani ba za a iya kai mutum Police station amma ina tabbatar muku cewa zamu sake shi, babu zancen zuwa Bompai kuma dan sandan da ya kama in bai yi sa’a ba ya bar aiki kenan. Zamu kare mutuncin ku, zamu kare darajar ku, zaben nan ko da tsiya-tsiya sai munci zaben nan.”
Idan ba a manta ba jihar Kano na daga cikin jihohin da za a gudanar da zaben a ranar 23 ga watan Maris.
Sauran jihohin da ba a kammala zaben gwamnan ba sun hada da Jihar, Filato, Bauchi, Adamawa, Sokoto da jihar Benuwai.
A jihar Kano abin yayi zafi da sai da aka rika kai ruwa rana tsakanin magoya bayan manyan jam’iyyun da ke fafatawa a zaben, wato APC da PDP.
A dalilin haka sai da ‘yan sanda suka tsare mataimakin gwamnan jihar Nasir Gawuna da kwamishinan Kananan hukumomin jihar, Sule Garu. Daga baya an sake su.
A sakamakon da aka riga aka bayyana, jam’iyyar PDP ce ke kan gaba da kuri’u sama da Miliyan daya.
An bayyana cewa kuri’un da aka soke sun fi yawan kuri’un da jam’iyyar PDP ta baiwa APC rata shine ya sa zaben bai kammalu ba.
Discussion about this post