Hukumar kwastam dake kula da shiyyar jihohin Barno da Yobe ta kama tirela dankare da buhunan shinkafa 300 a jihar Barno.
Shugaban shiyar Abdullahi Biu ya fadi haka da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ranar Laraba a Maiduguri.
Biu ya ce hukumar ta yi nasarar kama wadannan tirelan ne ranar biyar ga watan Maris a hanyar Bama-Banki.
Buhunan shinkafa,ridi, waken soya, sabulu, busashshen kifi da masara na daga cikin kayan da suka kama a wannan tirela.
Biu ya kuma kara da cewa aiyukkan Boko Haram bai hana hukumar yin aikin ta ba a wadannan yankuna.
” Sai dai har yanzu hukumar na samun matsaloli da yankin Gamboru-Banki da Gaidam saboda Boko Haram din.
Yace a bara hukumar ta sami nasarar yin kamen kayan da suka kai Naira miliyan 283.
Biu yace duk da haka hukumar za ta hada hannu da sauran jami’an tsaron dake shiyar domin kara sa himma samun nasara a ayyukkan ta.
Discussion about this post