Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta bayyana dalilan da suka sa ta ki amincewa ta bai wa kowane dan takarar Sanatan Jihar Imo ta Yamma satifiket na shaidar yin nasara.
Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe, Innocent Ibeabuchi, ya ce an tilasta shi ya fadi sunan Gwamna mai barin gado, Rochas Okorocha ne a matsayin wanda ya yi nasarar zaben Sanata na Shiyyar Imo ta Yamma.
“…An tare ni, aka hana ni fita tsawon kwanaki. Tilas ta sa zan bayyaya sakamakon, saboda barazanar da ake yi min, kuma ina son na bar wurin nan, na je na ga iyali na hankali na ya kwanta. Saboda haka a kan wannan dalilin ina mai bayyana wannan sakamkon a bisa tilas, ba da son rai na ba.”
Haka Ibeabuchi ya furta kafin ya bayyana sakamakon, wanda daga baya INEC ta kasa ta ki amincewa tunda sai da aka tilasta jami’in ta ya bayyana sakamakon da ba na gaskiya ba.
A cikin jerin sunayen zababbun sanatoci da INEC ta buga ranar Litinin da ta gabata, ta cire sunan Rochas Okorocha.
Maimakon sunan sa, sai INEC ta rubuta cewa: “An bayyana sakamakon sa a bisa tilastawa.”
Haka Kakakin Yada Labarai na INEC, Festus Okoye ya bayyana a wani shiri da aka yi da shina Gidan Talbijin na Channels.
Discussion about this post